Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Abin da Kifin Remora Yake Makalewa a Jikin Dabbobi da Shi

Abin da Kifin Remora Yake Makalewa a Jikin Dabbobi da Shi

 Remora wani irin kifi ne yake mannewa a jikin wasu kifaye ko dabbobin da ke cikin teku. Kuma yakan manne ko bar jikin kifin ko dabbar ba tare da ya yi mata lahani ba. Yadda kifin nan yana yin hakan, ya burge masu bincike sosai.

 Ka yi tunani a kan wannan: Kifin yana makalewa a jikin kifaye kamar su ray da shark da whale da kunkurun ruwa da dai sauransu, ko da fatarsu tana da tsantsi. Kifin remora yana cin kwayoyin cuta da abincin da dabbar ta ci ta rage. Ban da haka, kifin yana bin dabbar duk inda ta je kuma dabbar tana kāre shi. Masu bincike suna kokari su san yadda kifin yake makalewa gam a jikin wasu dabbobi ba tare da sun sani ba.

 Kifayen remora suna bin wani babban kifin da ake kira whale shark

 Abin da kifin remora yake amfani da shi ya makale a jikin wasu dabbobi yana kansa ne kuma yana kama da tire. A ta baki-bakin tiren, akwai soka mai kauri da kuma laushi, kuma da shi ne kifin yake mannewa a jikin dabba gam-gam. A cikin tire din kuma akwai kananan abubuwa da suka rarrabu kamar kunya-kunya da ba sa tankwarewa. Idan kananan abubuwan nan suka tashi tsaye, su suke mannewa a jikin dabbar kuma ba sa subulewa. Hakan yana sa kifin ya iya rike dabbar gam-gam kuma kome guduwar dabbar ko yadda take jujjuyewa, wannan kifin ba zai subule ba.

 Wannan tire da ke taimaka wa kifin remora ya manne a jikin wasu dabbobi ya burge ’yan kimiyya sosai, shi ya sa suka kera makamancinsa. Wannan na’urar da suka kera yana iya mannewa a jikin abubuwa dabam-dabam. Sa’ad da ’yan kimiyya suka yi kokarin balle na’urar daga jikin abin da suka manne shi, sun kasa duk da cewa sun yi amfani da karfi sosai!

 Fasahar da aka yi amfani da ita wajen kera wannan na’urar za ta iya taimakawa a fannoni da yawa, kamar a fannin yin na’urori da ake mannewa a jikin dabbobi da ke cikin teku idan ana so a yi nazari a kansu. Ban da haka, ana amfani da wannan fasahar wajen manne wuta ko wasu kayayyaki a karkashin gadoji ko kuma jiragen ruwa.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin yadda kifin remora yake makalewa a jikin dabbobi sakamakon juyin halitta ne? Ko halittarsa aka yi?