Koma ka ga abin da ke ciki

Ibadarmu ga Allah

Yin rayuwar da ta jitu da kaꞌidodin Littafi Mai Tsarki bai da sauki, amma shi ne zai taimaka mana mu yi rayuwa mai inganci ke nan. Ga yadda za ka iya yin hakan.

Belief in God

Matasa Suna Tattaunawa Game da Yin Imani da Allah

A wannan bidiyo mai tsawon minti uku, matasa sun bayyana abin da ya tabbatar musu cewa akwai Mahalicci.

Halitta ko Ra’ayin Bayyanau?​—Sashe na 1: Me Ya Sa Za Ka Yi Imani da Allah?

Za ka so ka dada karfin zuciya a bayyana dalilin da ya sa ka yi imani da Allah? Ka nemi taimako a kan yadda za ka ba da amsa idan wani ya yi maka tambaya game da abin da ka yi imani da shi.

Yadda Za A Kusaci Allah

Mene ne Amfanin Yin Addu’a?

Shin, ana yin addu’a ne don a ji sauki a zuciya kawai ko akwai wani dalili dabam?

Ta Yaya Za Ka Inganta Addu’o’inka?

Wannan shafin rubutu zai taimaka maka ka bincika abubuwan da kake fada sa’ad da kake addu’a da kyan addu’ar.

Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Rika Halartar Taro a Majami’ar Mulki?

Shaidun Jehobah suna halartar taro sau biyu kowane mako, a wurin da ake kira Majami’ar mulki. Me ake yi a wurin, kuma ta yaya za ka amfana yayin da kake halarta?

Ka Yi Koyi da Bayin Allah da Ke Littafi Mai Tsarki

Ka daraja abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarka da Allah!

A waɗanne hanyoyi musamman za ka iya nuna cewa kana daraja abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarka da Allah?

Ka Kāre Bauta ta Gaskiya!

A waɗanne fasalolin rayuwa ne za a nuna gaba gaɗi sosai idan an zo zancen sujjada?

Allah Ya Warkar da Hezekiya

Ka karanta wannan labarin Littafi Mai Tsarki don ka ga yadda za ka kyautata addu’o’inka.

An Cece Su Daga Tanderun Wuta!

Ka koya abin da ya sa yake da muhimmancin ka dage a kan abin da ka gaskata.

Allah Ya Amsa Addu’arsa

Ka bincika game da Nehemiya, ka ga yadda aka taimake shi ya yi tsayayya da ’yan hamayya

Za Ka Nuna Jin Kai Kuwa?

Ka yi nazarin misalin Ba-samariyi mai tausayi, kuma ka ga darussa da za ka koya.

Karatu da Nazarin Littafi Mai Tsarki

Matasa Sun Yi Magana Game da Karatun Littafi Mai Tsarki

Karatu bai da sauki, amma Karatun Littafi Mai Tsarki na da amfani. Matasa hudu sun bayyana yadda karatun Littafi Mai Tsarki yake sa su amfana.

Ta Yaya Littafi Mai Tsarki Zai Taimaka Mini?—Sashe Na Daya: Ka Bincika Littafi Mai Tsarki

In ka sami wani tsohon ƙaton akwati mai abubuwa masu tamani, ba za ka yi marmarin sanin abin da ke ciki ba? Littafi mai Tsarki yana kama da wannan akwatin. Yana dauke da abubuwa masu tamani.

Samun Ci-gaba a Ibada

Rayuwa Mafi Inganci

Za ka so ka yi rayuwa mai gamsarwa? A bidiyon nan, Cameron ta fadi yadda take jin dadin rayuwa a inda ba za ka zata ba.