Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya ce a rika bayarwa da son rai kuma a yi hakan don dalilin da ya dace. Ya nuna cewa wanda ya bayar da kuma wanda ya karba suna farin ciki. (Karin Magana 11:25; Luka 6:38) Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.”​—Ayyukan Manzanni 20:35.

 A wane lokaci ne bayarwa ke sa Allah farin ciki?

 Bayarwa tana sa Allah farin ciki sa’ad da aka yi hakan da son rai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowa ya bayar kamar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilas ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.”​—2 Korintiyawa 9:7.

 Allah yana amincewa da bayarwa da aka yi da zuciya daya. (Yakub 1:27) Mutumin da ke taimaka wa mabukaci yana faranta ran Allah, kuma Allah yana daukan irin wannan taimakon kamar ana ba shi rance ne. (Karin Magana 19:17) Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah zai biya mutumin.​—Luka 14:​12-14.

 Yaushe ne bayarwa ba ta dace ba?

 Idan ka yi hakan don son kai. Alal misali don:

  •   Ka burge mutane.​​—Matiyu 6:2.

  •   Ka sami wani abu.​​—Luka 14:​12-14.

  •   Ka sami rai na har abada.​—Zabura 49:​6, 7.

 Idan ka yi hakan don ka tallafa fa ma ayyuka ko halayen da Allah ya haramta. Alal misali, ba zai dace mu ba wani kudi don ya yi caca ko ya sha kwaya ko kuma ya sha giya ya bugu ba. (1 Korintiyawa 6:​9, 10; 2 Korintiyawa 7:1) Hakazalika, ba zai dace mu tallafa ma wani da zai iya biyan bukatunsa amma ya ki yin aiki ba.​—2 Tasalonikawa 3:10.

 Idan kana ba mutane kyauta sosai har ka mance da iyalinka. Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa wajibi ne magidanta su biya bukatun iyalinsu. (1 Timoti 5:8) Ba zai dace magidanci ya rika ba mutane kyauta sosai amma iyalinsa suna shan wahala. Hakazalika, Yesu ya koyar cewa bai dace mutane su ki kula da iyayensu da suka tsufa ta wajen da’awa cewa sun riga sun kebe dukiyarsu ga Allah ba.​—Markus 7:​9-13.