Koma ka ga abin da ke ciki

Allah Iko ne Marar-Siffa?

Allah Iko ne Marar-Siffa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Allah yana nuna iko wanda babu kamarsa a dukan sararin halitta. Game da yadda ya halicci biliyoyin taurari, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku tada idanunku sama, ku duba ko wanene ya halicci waɗannan, wanda ya kawo rundunansu bisa ga lissafinsu: yana kiransu duka da sunansu; bisa ga girman ikonsa, domin shi mai-ƙarfi ne cikin iko, ba wanda ba shi ko ɗaya.”—Ishaya 40:25, 26.

 Amma Allah ba wani iko ne kawai mai ƙarfi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce yana da jiyejiye, kamar ƙauna da kuma ƙiyayya. (Zabura 11:5; Yohanna 3:16) Ya kuma nuna cewa yadda mutane suke aikatawa yakan shafi Allah.—Zabura 78:40, 41.