Koma ka ga abin da ke ciki

Matsalolin Kudi da Cin Bashi—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimakawa Kuwa?

Matsalolin Kudi da Cin Bashi—Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimakawa Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Kwarai kuwa. Wadannan ka’idodin Littafi Mai Tsarki guda hudu da ke gaba za su iya taimake ka ka magance matsalolin kudi da kuma cin bashi:

  1.   Ka rubuta abin da za ka saya. “Tunanin mai-himma zuwa yalwata kadai su ke nufa: Amma kowane mai-garaje wajen tsiya yake nufa.” (Misalai 21:5) Kada ka yi garajen sayan wani abu don kawai yana da araha. Ka tsara yadda za ka kashe kudi kuma ka rika bin wannan tsarin.

  2.   Ka guji cin bashi da garaje. “Mai-cin bashi kuma bawa ne ga mai-bada bashi.” (Misalai 22:7) Idan ka riga ka ci bashi kuma ka kasa biya a lokacin da ya kamata, sai kai da wadanda ka ci bashi daga wurin su ku sake tsara yadda za ka biya bashin. Ka kokarta ka biya. Ka nuna hali irin na mutumin da aka kwatanta a littafin Misalai. Wurin ya ce: “Ka ƙasƙantar da kanka, ka yi roƙo ga maƙwabcinka: Kada ka ba idanunka barci.” (Misalai 6:1-5) Ko da an ki yarda ku sake tsarin, ka ci gaba da roko.

  3.   Kada ka so kudi ainun. “Mutum mai hadama yana gaggawar samun dukiya, bai kuwa sani ba, ashe, fatara ce za ta same shi.” (Misalai 28:22, Littafi Mai Tsarki) Hassada da hadama suna kai ga fatara. Kari ga haka, za su iya sa mutum ya yi banza da ibada.

  4.   Ka gamsu da abin da kake da shi. “Da ya ke muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (1 Timothawus 6:8) Kudi ba ya kawo farin ciki da gamsuwa. Wasu da suke farin ciki sosai a duniya ba masu dukiya ba ne. Abin da suke mora shi ne kaunar juna da suke yi a cikin iyali da abokai da kuma dangantakarsu da Allah.​—Misalai 15:17; 1 Bitrus 5:6, 7.