Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Mini Idan Ina Bakin Ciki Kuwa?

Littafi Mai Tsarki Zai Iya Taimaka Mini Idan Ina Bakin Ciki Kuwa?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 E, domin muna samun taimako mafi kyau daga wajen “Allah, shi da ke karfafa wa kaskantattu zuciya.”—2 Korintiyawa 7:6, Littafi Mai Tsarki.

Taimakon da Allah yake tanadar wa masu bakin ciki

  •   Karfin zuciya. Allah ba zai kawar da dukan matsalolin da kake fuskanta ba, amma zai “karfafa” ka ta wajen amsa addu’o’inka sa’ad da ka roke shi ya ba ka karfin jimrewa. (Filibiyawa 4:13) Za ka iya kasancewa da tabbaci cewa zai saurare ka, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji yana kusa da wadanda suka karai, Yakan ceci wadanda suka fid da zuciya.” (Zabura 34:18, LMT) Hakika, ko da ba ka iya furta ainihin yadda kake ji ba, Allah zai iya gane yanayinka.​—Romawa 8:26, 27.

  •   Misalai masu kyau. Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya yi wa Allah addu’a: “A cikin fid da zuciyata na yi kira gare ka.” Wannan mai zabura da ke bakin ciki ya sami karfafa sa’ad da ya tuna cewa Allah mai gafartawa ne sosai. Saboda haka, ya ce wa Allah: “Idan kana yin lissafin zunubanmu, Wa zai kubuta daga hukunci? Amma kakan gafarta mana, domin mu zama masu tsoronka.”—Zabura 130:1, 3, 4, LMT.

  •   Bege. Ban da ta’aziyya da yake yi mana yanzu, Allah ya yi alkawarin cewa zai cire dukan matsaloli da ke sa mu bakin ciki. Sa’ad da ya cika alkawarin nan, “ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.”​—Ishaya 65:17.

 Abin lura: Ko da yake Shaidun Jehobah suna dogara ga taimako da Allah yake yi, sukan nemi taimako daga likitoci domin ciwo kamar yin bakin ciki sosai. (Markus 2:17) Amma fa, ba ma gaya wa mutane irin jinyar da za su yi; muna ganin ya dace kowane mutum ya tsai da nasa shawara game da jinyar ya dace masa.