Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ake Nufi da Gafartawa?

Me Ake Nufi da Gafartawa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Gafartawa tana nufin yafe wa wanda ya yi mana laifi. A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar Hellenanci da aka fassara zuwa “gafartawa” tana nufin “ka bari ya wuce,” kamar yadda mutum ba zai tilasta a biya shi bashin da aka karba daga wurinsa ba. Yesu ya yi amfani da wannan kwatancin yayin da ya koya wa mabiyansa su yi addu’a cewa: “Ka gafarta mana zunubanmu; gama mu da kanmu kuma muna gafarta wa dukan wanda ya ke mabarcinmu.” (Luka 11:4) Hakazalika, a cikin misalin da ya bayar a kan bawa marar jin kai, Yesu ya kwatanta gafartawa da yafe bashi.—Matta 18:23-35.

 Idan muka gafarta wa mutane, ba za mu rike laifinsu a zuciya ba kuma ba za mu nace sai an biya mu diyyar hasarar da aka ba mu ba. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kauna ta kwarai ce za ta sa mutane su gafarta da dukan zuciyarsu, da yake kauna “ba ta riko.”—1 Korintiyawa 13:4, 5.

Abin da gafartawa ba ta nufi

  •   Yin na’am da laifi. Littafi Mai Tsarki ya yi tir da wadanda suke cewa munanan ayyuka suna da kyau.—Ishaya 5:20.

  •   Yi kamar laifin bai faru ba sam. Allah ya gafarta wa Sarki Dauda zunubi mai tsanani da ya yi amma bai kare shi daga sakamakon zunubinsa ba. Har ma Allah ya sa aka rubuta zunuban da Dauda ya aikata a cikin Littafi Mai Tsarki domin mu rika tunawa da su.—2 Sama’ila 12:9-13.

  •   Barin wasu su ci da guminka. A ce ka ara wa mutum kudi kuma ya yi cinye kudin sa’an nan ya kasa biyanka kamar yadda ya yi alkawari. Sai ya zo wurinka neman gafara. Za ka iya zaban ka gafarta masa ta wajen kin rike laifinsa a zuciya har ma ka yafe masa bashin. Amma kana iya kudura a zuciyarka cewa ba za ka kara ara masa kudi ba.—Zabura 37:21; Misalai 14:15; 22:3; Galatiyawa 6:7.

  •   Gafartawa bayan babu dalilin yin hakan. Allah ba ya gafarta wa mutanen da suka yi zunubi da gangan sa’an nan suka ki su karbi laifinsu ko kuma su canja halinsu ko su nemi gafara. (Misalai 28:13; Ayyukan Manzanni 26:20; Ibraniyawa 10:26) Irin mutanen nan da suka ki su tuba suna mai da kansu magabtan Allah kuma Allah ya ce kada mu gafarta ma wadanda ya ki ya gafarta musu.—Zabura 139:21, 22.

     Idan wani ya yi maka mugunta kuma ya ki ya nemi gafara ko ma ya amince da laifinsa fa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka dena yin fushi, ka rabu da hasala.” (Zabura 37:8) Ko da yake ba za ka ce ba a yi maka laifi ba, amma za ka iya daina yin fushi. Ka bar maganar a hannun Allah domin shi ne zai hukunta mutumin. (Ibraniyawa 10:30, 31) Kari ga haka, za ka iya samun karfafa idan ka tuna cewa a nan gaba, Allah zai sa ba za mu yi bakin ciki ko fushi kamar yadda muke yi a yanzu ba.—Ishaya 65:17; Ru’ya ta Yohanna 21:4.

  •   “Gafarta” kowane kuskure da muke gani an yi mana. A wasu lokatai, maimakon mu ce mun yafe wa mutane a kan kowane laifi da muke gani a yi mana, zai dace mu gaya wa kanmu tun da farko cewa bai kamata mu yi fushi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ka yi garaje a ranka garin yin fushi; gama wawa ke rike da fushi cikin zuciyarsa.”—Mai-Wa’azi 7:9.

Yadda za ka gafarta wa mutane

  1.   Ka tuna abin da gafartawa ta kunsa. Ba wai za ka yi kamar ba a yi maka laifi ba ko kamar babu abin da ya faru, amma kana barin laifin ya wuce ne kawai.

  2.   Ka tuna da amfanin gafartawa. Gafartawa da kin yin fushi zai kwantar maka da zuciya, ta inganta lafiyar jikinka kuma za ta sa ka dada farin ciki. (Misalai 14:30; Matta 5:9) Amma mafi muhimmanci shi ne, gafarta wa mutane zai sa Allah ya gafarta maka laifofinka.—Matta 6:14, 15.

  3.   Ka yi kokari ka fahimci yadda wasu suke ji. Dukanmu ajizai ne. (Yakub 3:2) Kamar yadda za mu ji dadi idan mutane suka gafarta mana, haka ma ya kamata mu ma mu gafarta ma wasu laifofinsu.—Matta 7:12.

  4.   Ka kasance da sanin yakamata. Idan laifin da aka yi mana bai taka kara ya karya ba, za mu iya bin wannan shawarar Littafi Mai Tsarki: “Kuna hakuri da juna.”—Kolosiyawa 3:13.

  5.   Ka dauki mataki nan da nan. Ka yi kokari ka gafarta nan da nan maimakon ka bar fushi ya rika dadewa a zuciyarka.—Afisawa 4:26, 27.