Koma ka ga abin da ke ciki

Shin, Allah Yana Canja Zuciyarsa?

Shin, Allah Yana Canja Zuciyarsa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Hakika, yakan canja zuciyarsa idan mutane suka canja halinsu. Alal misali, sa’ad da Allah ya aika sakon hukunci ga mutanen Isra’ila ta dā, ya ce musu: ‘Watakila za su ji, kowane mutum kuma shi juyo ga barin mugun halinsa: domin in juya ga barin masifa da na nufa in yi musu, saboda muguntar ayyukansu.’—Irmiya 26:3.

 Yawancin juyin Littafi Mai Tsarki sun fassara wannan ayar cewa, Allah ya “tuba” daga masifar da ya nufi mutane da ita, kuma hakan zai sa a dauka cewa kamar Allah ya yi kuskure ne. Amma, ainihin kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita tana iya nufin “canja zuciya ko kuma nufi.” Wani masani ya ce: “Allah yana canja hukuncinsa idan mutane suka canja halinsu.”

 Amma, ba dole ne Allah ya canja zuciyarsa domin zai iya canjawa ba. Ka yi la’akari da wadannan misalai a cikin Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa Allah bai canja zuciyarsa ba:

  •   Allah bai bar Balak ya sa Shi ya canja zuciyarsa don ya la’anta Isra’ila ba.—Littafin Lissafi 23:18-20.

  •   Sa’ad da Sarki Saul ya dukufa wajen yin mugunta, Allah ya ki ya canja zuciyarsa game da cire shi daga sarauta.—1 Sama’ila 15:28, 29.

  •   Allah zai cika alkawarin da ya yi na nada Dansa ya zama Firist har abada. Allah ba zai canja zuciyarsa ba.—Zabura 110:4.

Amma ba Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ba ya canjawa ba?

 Hakika, a cikin Littafi Mai Tsarki Allah ya ce: “Ni Ubangiji ba mai sakewa ba ne.” (Malakai 3:6) Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya rubuta cewa Jehobah Allah ne “wanda sakewa ba ta yiwuwa gare shi” kamar “inuwa.” (Yakub 1:17) Amma, hakan bai karyata abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa Allah ba ya canjawa ba. Allah ba ya canjawa domin halinsa da ka’idodinsa a kan kauna da adalci ba sa canjawa. (Kubawar Shari’a 32:4; 1 Yohanna 4:8) Duk da haka, yana iya canja umurnin da yake ba mutane a lokaci dabam-dabam. Alal misali, Allah ya ba Sarki Dauda umurni dabam-dabam a yake-yake guda biyu da ya yi, amma dukan umurnin da ya bayar sun kawo nasara.—2 Sama’ila 5:18-25.

Allah yana da-na-sani ne don ya halicci ’yan Adam?

 A’a, amma ransa ya bace domin yawancin mutane sun ki shi. Game da yanayin duniya kafin Rigyawa a zamanin Nuhu, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji fa ya tuba da ya yi mutum a duniya, abin ya bata masa zuciya kwarai.” (Farawa 6:6) A wannan ayar, an dauko kalmar nan “tuba” daga kalmar Helenanci da ke nufin “canja zuciya.” Allah ya canja zuciyarsa game da yawancin mutane da suka rayu kafin Rigyawa domin sun zama miyagu. (Farawa 6:5, 11) Ko da yake ransa ya bace sosai domin sun zabi su yi mugunta, bai canja zuciyarsa game da dukan mutane ba. Ya kāre zuriyar ’yan Adam daga Rigyawar ta wurin Nuhu da iyalinsa.​—Farawa 8:21; 2 Bitrus 2:5, 9.