Koma ka ga abin da ke ciki

Iblis ne Tushen Dukan Shan Wahala?

Iblis ne Tushen Dukan Shan Wahala?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa Shaiɗan Iblis yana da rai kamar mutum, yana kama da mugun shugaba da ke nace a yi nufinsa ta wurin “alamu . . . na ƙarya” da kuma “ruɗami.” Hakika, “ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske,” in ji Littafi Mai Tsarki. (2 Tassalunikawa 2:9, 10; 2 Korinthiyawa 11:14) Ana sanin kasancewar Iblis ta wurin ɓarna da yake yi ne.

 Amma dai, ba Iblis ne ke da alhakin dukan wahala da ake sha ba. Me ya sa? Allah ya halicci mutane da baiwar su iya yin zaɓe tsakanin nagarta da mugunta. (Joshua 24:15) Idan muka yi mugun zaɓe za mu sha azabarsa.—Galatiyawa 6:7, 8.