Koma ka ga abin da ke ciki

20 GA DISAMBA, 2019
ARGENTINA

Taron Kasashe na 2019 a Buenos Aires, Ajantina

Taron Kasashe na 2019 a Buenos Aires, Ajantina
  • Kwanan Wata: 13-15 ga Disamba, 2019

  • Wurin Taro: Estadio Único de La Plata, Buenos Aires, Ajantina

  • Yaruka da Aka Yi Taron: Yaren Kurame na Amirka, Turanci, Sifanisanci

  • Adadin Mahalarta: 47,555

  • Wadanda Aka Yi wa Baftisma: 563

  • Mutane Daga Wasu Kasashe: 6,300

  • Kasashensu: Bolivia, Amirka ta Tsakiya, Turai na Tsakiya, Chile, Czech-Slovak, Finland, Italiya, Koriya, Paraguay, Peru, Romaniya, Scandinavia, Sifen, Amirka.

  • Labarai: Maria Anapios, manajar cinikayya na Panamericano Hotel inda mahalarta suka sauka ta ce: “A wannan lokaci da akwai sabani tsakanin kabilu da kasashe da kuma duniya baki daya, ganin irin wannan taron yana da muhimmanci sosai domin misali ne na ’yan’uwantaka da salama da kuma kauna da muke bukata sosai.

 

ʼYan’uwa suna marabtar baki a tashar jirgin sama

ʼYan jarida suna ganawa da ʼyan’uwa hudu kafin a soma taron

ʼYan’uwa maza da mata suna zuwa wurin taron

Mahallara suna tafi bayan an kammala wani jawabi

An yi wa sababbi baftisma a tafki da ke wurin taron

Dan’uwa Kenneth Cook, memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu yana yin jawabi na karshe a ranar Lahadi

Wasu ’yan’uwa mata suna daukan hoto kuma suna rike da haruffan nan “LOVE,” wato kauna

Mahallara suna daukan hoto

’Yan’uwan da ke hidima ta cikakken lokaci da suka halarci taron suna gai da ’yan’uwa sa’ad da aka tashi taron a ranar Lahadi

’Yan’uwan da ke yanki suna yi wa ’yan’uwan da suka halarci taron wasannin a liyafar da yamma