Koma ka ga abin da ke ciki

Hoton da aka dauka daga sarari na Cyclone Yasa da tsibiran Fiji da guguwar ta shafa

7 GA JANAIRU, 2021
FIJI

Mahaukaciyar Guguwar Yasa Mai Mataki Biyar Ta Yi Barna a Fiji

Mahaukaciyar Guguwar Yasa Mai Mataki Biyar Ta Yi Barna a Fiji

Inda ya faru

Fiji

Bala’i

  • A ranar 17 ga Disamba, 2020, wata guguwa mai tsanani da ake kira Yasa ta yi barna a tsibiri na biyu da ya fi girma a Fiji, wato tsibirin Vanua Levu

  • Yasa ce guguwa ta biyu mafi girma da ta taba aukuwa a Fiji. Mai yiwuwa guduwar iskar ya kai kilomita 260 a cikin awa daya (ko mil 161 a cikin awa daya)

  • Akalla ikilisiyoyi da rukunoni 30 ne ke wannan yankin

Yadda ya shafi ’yan’uwanmu

  • Babu dan’uwa ko ’yar’uwa da ta ji rauni

  • Rahotannin da aka fara samuwa sun nuna cewa iyalai 20 sun gudu sun bar gidajensu

  • Guguwar ta lalata gonaki da yawa, kuma musamman daga gonakin ne masu shela 430 da suke zama a yankin suke samun abinci

Abubuwan da aka yi hasararsu

  • Gidaje 10 sun rushe

  • Gidaje 25 sun lalace

  • Majami’ar Mulki guda 1 ya dan lalace

Agaji

  • Reshen ofishinmu na Fiji ya kafa Kwamitin Agaji guda uku. Wadannan kwamitin agajin sun tanadar abubuwa kamar ruwan sha mai kyau da riguna da abinci da tampolin wa masu shelar da bala’in ya shafa. Kari ga haka, kwamitin sun samar ma wadanda suka rasa gidajensu matsuguna

  • Wakilai daga ofishinmu na Fiji tare da masu kula da da’ira da ke yankin suna kai ziyarar karfafa ga ’yan’uwan da bala’in ya shafa

  • Duka ’yan’uwa da suke ba da agaji da kuma kai ziyarar karfafa suna bin ka’idodin kāriya da aka kafa don cutar koronabairas

Ko da yake ’yan’uwanmu sun yi hasara saboda wannan mummunar guguwar, sun yarda da kalmomin da ke Zabura 46:1 cewa: “Allah shi ne wurin buyanmu.”