Koma ka ga abin da ke ciki

14 GA SATUMBA, 2017
INDIYA

Ruwan sama mai karfi da ake kira Monsoon ya yi barna sosai a Mumbai

Ruwan sama mai karfi da ake kira Monsoon ya yi barna sosai a Mumbai

A ranar 28 ga Agusta, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Mumbai a Indiya. Hakan ya sa mutane 14 sun rasa rayukansu.

An sami rahoto daga ofishin Shaidun Jehobah da ke Indiya cewa babu wani dan’uwa da ya ji rauni ko kuma ya rasa ransa. Amma ambaliya ta lalata gidajen Shaidu da yawa. Shaidun Jehobah da ke kasar suna kokarin tanadin abinci kuma suna shasshare gidajen da ambaliyar ta lalata.

Ofishin Shaidun Jehobah da ke kasar tana tallafa wa ‘yan’uwan da ke Mumbai da kuma sauran wuraren da ambaliyar ta shafa a Indiya.

Media Contacts:

International: David A. Semonian, Office of Public Information, +1-845-524-3000

India: Tobias Dias, +91-9845476425