Koma ka ga abin da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyin Littafi Mai Tsarki

Zai yiwu a gafarta mana zunubanmu kuwa?

Yin abin da zai faranta wa Allah rai ba abu mai wuya ba ne

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan ’yan Adam ajizai ne. Mun gāji wannan ajizancin daga mutum na farko, wato Adamu. Shi ya sa mukan yi wasu abubuwa marasa kyau kuma daga baya mu yi da-na-sani. Amma Yesu Kristi, Dan Allah, ya ba da ransa don a gafarta mana zunubanmu. Hadayar da ya yi ta sa Allah zai iya gafarta zunubanmu. Wannan kyauta ce daga Allah.​—⁠Karanta Romawa 3:​23, 24.

Wasu mutane sun yi zunubai masu tsanani kuma hakan ya sa suna shakka ko Allah zai gafarta musu. Amma abin farin cikin shi ne, Kalmar Allah ta ce: ‘Jinin Yesu Dansa yana tsabtace mu daga dukan zunubi.’ (1 Yohanna 1:⁠7) Jehobah yana a shirye ya gafarta wa mutum ko da ya yi zunubi mai tsanani, idan har ya tuba da gaske.​—⁠Karanta Ishaya 1:⁠18.

Mene ne za mu yi don a gafarta mana?

Idan muna so Allah ya gafarta mana, muna bukatar mu koya game da shi, wato mu san hanyoyinsa da shawarwarinsa da kuma ka’idodinsa. (Yohanna 17:⁠3) A koyaushe, Jehobah yana gafarta ma wadanda suka tuba kuma suka yi kokarin canja halinsu.​—⁠Karanta Ayyukan Manzanni 3:⁠19.

Yin abin da zai faranta wa Allah rai ba abu mai wuya ba ne domin Jehobah ya san kasawarmu. Shi mai jin kai ne, mai alheri kuma. Ba shakka, za ka so ka koyi yadda za ka faranta wa Allah rai domin kaunarsa da alherinsa.​—⁠Karanta Zabura 103:​13, 14.