Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 26

’Yan Leken Asiri

’Yan Leken Asiri

Isra’ilawa sun bar Dutsen Sinai kuma suka bi cikin jejin Paran har suka iso wani gari da ake kira Kadesh. Sai Jehobah ya gaya wa Musa: ‘Ka zaɓi maza 12 su tafi Kan’ana, ƙasar da nake son in ba ku, don su leƙa asirinta.’ Sai Musa ya zaɓi maza 12 kuma ya ce musu: ‘Ku tafi ƙasar Kan’ana don ku dubo mana ko ƙasar tana da kyau don noma. Ku duba ko mutanen suna da ƙarfi ko a’a ko kuma suna zama a tanti ne ko kuma birane.’ Sai ’yan leƙen asirin su 12, Joshua da Kaleb ma suna cikinsu, suka kama hanyar zuwa ƙasar Kan’ana.

Bayan kwana 40, sai ’yan leƙen asirin suka dawo da ’ya’yan itacen ɓaure da rumana da kuma anab. Kuma suka ce: ‘Ƙasar tana da kyau amma mutanen suna da ƙarfi sosai kuma suna da katanga masu tsawo.’ Sai Kaleb ya ce: ‘Za mu iya yaƙar su. Mu tafi nan da nan!’ Ka san dalilin da ya sa Kaleb ya gaya musu haka? Domin shi da Joshua sun dogara ga Jehobah. Amma sauran ’yan leƙen asirin suka ce: ‘Ba gaskiya ba ne! Mutanen manya-manya ne! Mu kamar fari ne a gaban su.’

Isra’ilawan sun ji tsoro. Sai suka yi gunaguni suna cewa: ‘Bari mu zaɓi wani shugaba kuma mu koma ƙasar Masar. Me ya sa za mu je ƙasar Kan’ana don a kashe mu?’ Da Joshua da Kaleb suka ji haka sai suka ce: ‘Kada ku yi wa Allah rashin biyayya kuma kada ku ji tsoro. Jehobah zai taimaka mana.’ Amma Isra’ilawan sun ƙi su saurare su kuma suka nemi su kashe Joshua da Kaleb!

Mene ne Jehobah ya yi? Sai ya gaya wa Musa cewa: ‘Har ila Isra’ilawa suna mini rashin biyayya duk da abubuwan da na yi musu? To, za su yi shekaru 40 suna yawo a jeji kuma a wurin za su mutu. Sai yaransu da Joshua da kuma Kaleb ne kaɗai za su shiga ƙasar da na ce zan ba su.’

“Don me kuka tsorata, ku masu-ƙanƙantar bangaskiya?”​—Matta 8:⁠26