Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA BIYAR

Ta Kāre Bayin Allah

Ta Kāre Bayin Allah

1-3. (a) Me ya sa Esther ta ji tsoron zuwa wajen mijinta? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna game da Esther?

ESTHER ta yi ƙoƙari ta kwantar da hankalinta yayin da ta kusan isa fādar sarki a birnin Shushan. Amma, yin hakan ba abu mai sauƙi ba ne. Yaya wannan fādar take? Tana da ban razana sosai. An zana hotunan bijimai masu fikafikai da maharba da zakuna a bangwaye masu launi iri-iri. An gina ginshiƙai da kuma manya-manyan mutum-mutumi. Daular tana kan Tudun Zagros kuma ta fuskanci kogin Choaspes. An gina ta a wurin ne domin ta tuna wa baƙi cewa sarkin da ke zama a wurin yana da iko sosai kuma wurin da Esther za ta ke nan. Shi maigidanta ne.

2 Maigidanta? Ahasuerus ba irin mijin da budurwa Bayahudiya mai aminci za ta so ta aura ba! * Bai yi koyi da mutane kamar Ibrahim ba, wanda ya nuna tawali’u kuma ya bi umurnin Allah cewa ya saurari matarsa Saratu. (Far. 21:12) Da kyar in sarkin ya san Allahn da Esther take bauta wa ko kuma Dokokinsa. Ahasuerus ya san dokokin ƙasar Farisa, haɗe da wadda ta haramta abin da Esther take gab da yi. Mene ne ke nan? Dokar ta ce a kashe duk mutumin da ya bayyana a gaban sarkin Farisa, idan bai gayyace shi ba. Sarkin bai gayyaci Esther ba, amma ga shi ta nufa wajensa. Yayin da take kusa da farfajiyar inda sarkin zai hange ta daga karagarsa, ƙila ta yi zato cewa za a kashe ta.—Karanta Esther 4:11; 5:1.

3 Me ya sa Esther ta yi ƙuru haka? Kuma mene ne za mu iya koya daga bangaskiyar wannan macen kirki? Bari mu fara tattauna yadda Esther ta zama sarauniya a ƙasar Farisa.

Yadda Aka Yi Rainon Esther

4. Wace ce Esther, kuma me ya sa ta soma zama da Mordekai?

4 Esther marainiya ce. Ba mu da cikakken bayani game da iyayenta waɗanda suka sa mata suna Hadassah. Hadassah sunan wani itace mai fararen furani masu kyau ne a Ibrananci. Sa’ad da iyayen Esther suka rasu, sai wani danginsu mai suna Mordekai ya ɗauki riƙon ta. Shi ɗan kawunta ne, amma ya girme ta sosai. Ya kawo ta gidansa kuma ya kula da ita kamar ’yarsa.—Esther 2:5-7, 15.

Mordekai yana da dalili mai kyau na yin alfahari da ɗiyarsa

5, 6. (a) Yaya Mordekai ya yi rainon Esther? (b) Wane irin aiki ne suke yi a Shushan?

5 Mordekai da Esther Yahudawa ne kuma suna zaman bauta a babban birnin Farisa. Wataƙila ’yan ƙasar sun ƙi jininsu domin Dokar da suke bi da kuma Allahn da suke bauta wa dabam ne. Babu shakka, Esther ta kusaci ɗan kawunta yayin da yake koya mata game da Jehobah, Allah mai jin ƙai da kuma rahama wanda ya cece su daga matsaloli a dā kuma yana gab da sake yin hakan. (Lev. 26:44, 45) Hakika, dangantakar Esther da Mordekai tana da ɗanko sosai.

6 Mordekai yana aiki a fādar sarki da ke Shushan. Shi da wasu bayin sarkin suna zama a kai a kai a ƙofar fādar. (Esther 2:19, 21; 3:3) Ba mu san irin aikin da Esther take yi ba sa’ad da take matashiya, amma wataƙila ita ce ke kula da Mordekai da kuma masaukinsu da ke hayin kogi kusa da fādar sarkin. Ƙila tana son zuwa kasuwar birnin Shushan, inda ake sayar da zinariya da azurfa da kuma wasu kayayyaki. Esther ba ta san cewa a nan gaba za ta samu waɗannan abubuwan rututu ba.

‘Mai Kyaun Gani’

7. Me ya sa aka ƙi da Vashti a matsayin sarauniya, kuma me ya faru bayan haka?

7 Wata rana, sai gulma ta yaɗu kamar wutar daji a fādar sarki. Ahasuerus ya yi wani babban biki inda aka yi ruwan abinci da inabi kuma sarkin ya sa aka kira sarauniyarsa Vashti wadda take wani ɓangare tare da matan fādar, amma ta yi ko-in-kula. Hakan ya ɓata wa sarkin rai ainun, sai ya nemi shawara a kan yadda zai koya wa Vashti hankali. Wace shawara ce aka ba shi? An shawarce shi ya kore ta daga fādarsa, kuma abin da ya yi ke nan. Bayan haka, sai bayin sarkin suka soma cigiyar budurwai masu kyau sosai a ƙasar baki ɗaya, domin sarkin ya zaɓi wadda za ta zama sarauniyarsa.—Esther 1:1–2:4.

8. (a) Me ya sa wataƙila Mordekai ya ɗan damu sa’ad da Esther ta yi girma? (b) Ta yaya za mu iya bin shawarar da ke Littafi Mai Tsarki game da sifarmu? (Ka duba Misalai 31:30.)

8 Ka kwatanta a zuci yadda Mordekai yake kallon Esther a kai a kai cike da farin ciki, yana kuma ɗan fargaba domin ta yi girma ta zama kyakkyawa. Littafi Mai Tsarki ya ce “yarinyar kuwa kyakyawa ce mai-kyaun gani.” (Esther 2:7) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya kamata namiji ko tamace mai kyau ta kasance da hikima da kuma tawali’u. Idan ba haka ba, mutumin zai zama mai fahariya da wasu munanan halaye. (Karanta Misalai 11:22.) Shin ka amince da hakan? Wane irin hali ne Esther take da shi duk da yake ita kyakkyawa ce? Fahariya ko tawali’u? Bari mu gani.

9. (a) Me ya faru sa’ad da bayin sarkin suka lura da Esther, kuma me ya sa bai kasance da sauƙi ta rabu da Mordekai ba? (b) Me ya sa Mordekai ya ƙyale Esther ta auri mai bautar gumaka? (Ka haɗa da akwatin.)

9 Bayin sarkin da ke cigiya sun lura da Esther. Sai suka ɗauke ta daga wajen Mordekai kuma suka kai ta fādar sarki a hayin kogi. (Esther 2:8) Hakika, bai kasance wa Esther da Mordekai da sauƙi su rabu da juna ba, domin dangantakarsu kamar ta uba da ’ya ce. Mordekai ba zai so ɗiyarsa ta auri mai bautar gumaka ba, ko da shi sarki ne, amma al’amarin ya fi ƙarfinsa. * Babu shakka, Esther ta saurari shawarar da Mordekai ya ba ta kafin a tafi da ita. Ta yi tunani dabam-dabam yayin da suke hanya zuwa Shushan. Yaya rayuwa za ta kasance mata a wurin?

“Ta Sami Tagomashi a Wurin Dukan Waɗanda Suka Gan Ta”

10, 11. (a) Ta yaya sabon wurin da Esther take zai iya shafanta? (b) A wace hanya ce Mordekai ya nuna cewa yana kula da Esther?

10 Rayuwar Esther ta canja baki ɗaya. Tana cikin “’yan mata da yawa” da aka tattara a ƙasar Farisa baki ɗaya. Babu shakka, al’adarsu da yarensu da halayensu sun bambanta sosai. Sarkin ya ce wani mai suna Hegai ya kula da su kuma a yi musu kwalliya sosai na tsawon shekara guda tare da tausa da māi. (Esther 2:8, 12) Irin wannan kwalliyar za ta iya sa ’yan matan su soma gasa da juna. Shin hakan ya shafi Esther kuwa?

11 Babu wani a duniya da ya damu da Esther kamar Mordekai. Littafi Mai Tsarki ya ce yana zuwa gidan kowace rana don ya san yadda Esther take. (Esther 2:11) Babu shakka, Mordekai ya yi alfahari sa’ad da wataƙila wani bawa da ke aiki a gidan matan ya ba shi labarin Esther. Me ya sa?

12, 13. (a) Yaya mutane suke ɗaukan Esther? (b) Me ya sa Mordekai zai yi farin ciki domin Esther ba ta fallasa yarenta ba?

12 Esther ta burge Hegai sosai har ya yi mata alheri. Ya sa mata bakwai su kula da ita kuma ya saka ta a wuri mafi kyau na gidan. Labarin ya ce: “Esther kuwa ta sami tagomashi a wurin dukan waɗanda suka gan ta.” (Esther 2:9, 15) Shin kyaun sifa ne kawai ya sa mutane suke yin sha’awar Esther? Ko kaɗan.

Esther ta san cewa tawali’u da hikima sun fi kyaun sifa muhimmanci

13 Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Esther kuwa ba ta rigaya ta bayana asalinta ba ko danginta; gama Mordekai ya rigaya ya umurce ta kada ta bayana.” (Esther 2:10) Mordekai ya dokace ta kada ta gaya wa kowa cewa ita Bayahudiya ce, wataƙila domin an ƙi jinin Yahudawa a daular Farisa. Mordekai ya yi matuƙar farin ciki domin Esther ta kasance da hikima da biyayya duk da yake ba ya tare da ita.

14. Ta yaya matasa a yau za su iya yin koyi da Esther?

14 Matasa a yau za su iya sa iyaye da kuma masu rainonsu farin ciki. Za su iya ƙin yin koyi da miyagu ko da suna nesa da iyayensu. Me ya sa? Domin idan sun yi koyi da Esther, za su faranta ran Ubansu da ke sama, wato Jehobah.Karanta Misalai 27:11.

15, 16. (a) Mene ne Esther ta yi don sarkin ya so ta? (b) Me ya sa sabon yanayin da Esther take ciki bai kasance mata da sauƙi ba?

15 Sa’ad da lokaci ya yi da Esther za ta bayyana a gaban sarki, an ba ta zarafin zaɓar abubuwan da take so, wataƙila kayan kwalliya. Amma ta bi shawarar Hegai, kuma ba ta bukaci fiye da abubuwan da ya gaya mata ba. (Esther 2:15) Esther ta san cewa ba kyaun sifa kaɗai ba ne zai sa sarkin ya amince da ita ba, amma tana bukatar filako da kuma tawali’u domin waɗannan halayen ba gama gari ba ne a fādar. Shin ta yi nasara kuwa?

16 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sarki kuwa ya ƙaunaci Esther gaba da dukan matan, ta kuwa sami tagomashi da alheri a wurinsa gaba da dukan ’yan budurwai; har ya sanya wa kanta kambin sarauta, ya maishe ta sarauniya maimakon Vashti.” (Esther 2:17) Babu shakka, ya yi wa wannan Bayahudiyar wuya ta saba da wannan sabon yanayi. Esther ta zama sarauniyar Sarki mafi iko a duniya a lokacin! Shin ta yi girman kai domin ita ce sarauniya yanzu? A’a!

17. (a) A waɗanne hanyoyi ne Esther ta yi biyayya ga Mordekai? (b) Me ya sa misalin Esther abin koyi ne a yau?

17 Esther ta ci gaba da yin biyayya ga Mordekai. Ba ta gaya wa kowa cewa ita Bayahudiya ce ba. Bugu da ƙari, sa’ad da Mordekai ya samu labarin maƙarƙashiyar da ake wa Ahasuerus, Esther ta yi biyayya kuma ta gaya wa sarkin. A sakamako, masu maƙarƙashiyar ba su yi nasara ba. (Esther 2:20-23) Ta kuma nuna imani ga Allahnta ta wajen yin biyayya da kuma tawali’u. Yana da muhimmanci sosai mu yi koyi da misalin Esther domin mutane da yawa a yau suna rashin biyayya da kuma tawaye. Amma mutane masu bangaskiya sosai suna yin biyayya kamar yadda Esther ta yi.

An Gwada Imanin Esther

18. (a) Mene ne wataƙila ya sa Mordekai ya ƙi rusuna wa Haman? (Ka kuma duba hasiya.) (b) Ta yaya maza da mata masu imani a yau suke yin koyi da misalin Mordekai?

18 An danƙa wa Haman wani babban matsayi a fādar Ahasuerus. Sarkin ya naɗa shi a matsayin firayim minista. Haman ne zai riƙa ba sarki shawara kuma shi ne mutum mafi iko na biyu a daular. Sarkin ya ma ce duk mutumin da ya ga Haman ya rusuna masa. (Esther 3:1-4) Amma bin wannan dokar ba ta kasance wa Mordekai da sauƙi ba. Yana biyayya ga sarkin idan dokarsa ba ta saɓa wa ta Allah ba. Haman Ba-agagi ne. Hakan yana nufin cewa shi dangin Agag sarkin Amalakawa wanda annabi Sama’ila ya kashe ne. (1 Sam. 15:33) Amalakawa mugaye ne sosai har suka zama maƙiyan Jehobah da kuma Isra’ilawa. Jehobah yana son a kashe Amalakawa baki ɗaya. * (Deut. 25:19) Yaya za a yi Bayahude mai aminci ya rusuna wa Ba’amalak? Mordekai ya ƙi yin hakan. Har wa yau, maza da mata masu imani sun yi kasada da ransu don su bi ƙa’idar nan: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—A. M. 5:29.

19. Mene ne Haman yake so ya yi kuma ta yaya ya rinjayi sarki?

19 Haman ya fusata ƙwarai. Ba Mordekai ne kaɗai yake so ya kashe ba, amma yana so ya halaka mutanensa baki ɗaya. Haman ya shafa wa Yahudawa kashin kaza a gaban sarki. Haman ya ce Yahudawa “wata al’umma a warwatse” ce, don ya nuna cewa ba su da wani muhimmanci ga sarki. Ƙari ga haka, ya ce Yahudawa ’yan tawaye ne don sun taka dokokin sarki. Haman ya ce zai biya duk kuɗin da ake bukata don a halaka dukan Yahudawa da ke daular. * Ahasuerus ya ba Haman hatimin sarki don ya hatimce duk umurnin da yake so.—Esther 3:5-10.

20, 21. (a) Ta yaya saƙon Haman ya shafi Mordekai da Yahudawa da ke Daular Farisa baki ɗaya? (b) Mene ne Mordekai ya roƙi Esther ta yi?

20 Ba da daɗewa ba, sai mahaya suka soma tafiya ɓangarori dabam-dabam na birnin don su yi shelar saƙon halaka Yahudawa. Yahudawan da suka dawo daga ƙasar Babila suna fama su sake gina ganuwar Urushalima kuma ba su da tsaro. Yaya kake ganin suka ji sa’ad da saƙon ya isa wurinsu? Wataƙila, sa’ad da Mordekai ya ji labarin, ya yi tunanin Yahudawa da ke Urushalima da abokansa da kuma danginsa da ke Shushan. Cike da baƙin ciki, Mordekai ya tuɓe rigarsa, ya sanya tsummoki kuma ya zuba toka a kansa, sai ya ta da muryarsa da kuka a tsakiyar birnin. Mene ne Haman ya yi a wannan lokacin? Shin ya ji tausayin Yahudawa da kuma abokansu da ke Shushan kuwa? Ina! Ya je yana shan inabi tare da sarkin.Karanta Esther 3:12–4:1.

21 Mordekai ya san cewa ya kamata ya ɗauki mataki. Amma, wane mataki ne zai iya ɗauka? Esther ta samu labarin yadda Mordekai yake baƙin ciki, sai ta aika masa tufafi, amma hakan bai ƙarfafa shi ba. Wataƙila ya daɗe yana mamakin dalilin da ya sa Jehobah ya ƙyale sarki mai bautar gumaka ya auri Esther. Amma yanzu, ya soma sanin dalilin. Mordekai ya aika saƙo ga sarauniya Esther. Wane saƙo ke nan? Ya ce ta roƙi sarkin ya ɗauki mataki “domin al’ummarta.”—Esther 4:4-8.

22. Me ya sa Esther take jin tsoron zuwa wajen mijinta? (Ka kuma duba hasiya.)

22 Babu shakka, Esther ta ji tsoro sa’ad da ta sami saƙon Mordekai. Wannan ne gwaji mafi girma da ta taɓa fuskanta. Saƙon da ta aika wa Mordekai ya tabbatar da hakan. Ta tuna masa dokar sarkin. Idan kowane mutum ya shiga wurin sarki ba tare da ya gayyace shi ba, za a kashe shi. Sai idan sarkin ya miƙa kandarinsa ne za a yafe wa mutumin da ya taƙa dokar. Esther ba ta sa rai cewa sarkin zai gafarce ta ba, musamman ma don abin da ya faru da Vashti sa’ad da ta ƙi amsa kiran sarki. Esther ta gaya wa Mordekai cewa ya kai kwanaki 30 da sarkin bai gayyace ta wurinsa ba. Ta yi tunani ko sarkin ya daina sonta da yake ya daɗe da bai ganta ba. *Esther 4:9-11.

23. (a) Mene ne Mordekai ya ce don ya ƙarfafa Esther? (b) Me ya sa ya kamata mu yi koyi da Mordekai?

23 Mordekai ya amsa Esther da gaba gaɗi don ya ƙarfafa bangaskiyarta. Ya gaya mata cewa idan ba ta ɗauki mataki ba, Jehobah zai aiki wani ya cece su. Amma, ba za a yi mata rangwame ba idan an zartar da dokar. Mordekai ya kasance da bangaskiya sosai ga Jehobah wanda ba zai taɓa ƙyale a halaka bayinsa ba kuma nufinsa ya bi ruwa. (Josh. 23:14) Sai Mordekai ya tambayi Esther, ya ce: “Wa ya sani ko domin wannan irin lokaci ne kin sami sarauta?” (Esther 4:12-14) Ya kamata mu yi koyi da Mordekai domin ya dogara baki ɗaya ga Jehobah. Shin kai ma kana yin hakan kuwa?—Mis. 3:5, 6.

Imaninta Ya Ɗara Tsoron Mutuwa

24. Ta yaya Esther ta nuna bangaskiya da gaba gaɗi?

24 Lokaci ya yi da Esther za ta ɗauki mataki. Ta gaya wa Mordekai cewa ya aririce ’yan’uwanta Yahudawa su yi azumi na kwana uku tare da ita. Bayan haka, sai ta furta kalmomin da suka nuna cewa tana da bangaskiya da kuma gaba gaɗi sosai. Ta ce: “Idan na halaka, na halaka ke nan.” (Esther 4:15-17, Littafi Mai Tsarki) Babu shakka, ta yi addu’a sosai fiye da yadda take yi a dā. Sai ta saka tufafinta mafi kyau kuma ta yi kwalliya sosai don ta shiga idon sarkin. Bayan haka, sai ta shiga wurinsa.

Esther ta sadaukar da ranta don ta kāre bayin Allah

25. Ka bayyana abin da ya faru sa’ad da Esther ta shiga fādar mijinta.

25 Esther ta shiga fādar sarki kamar yadda aka bayyana a sakin layi na farko. Ka yi tunanin irin tsoron da take ji da kuma yadda take addu’a yayin da take shiga wurin, har ta hangi Ahasuerus a kan karagarsa. Wataƙila ta kalle shi don ta ga yanayin fuskarsa. Idan ta jira a wurin, za ta ji kamar lokaci ba ya tafiya. Amma mijinta ya hango ta. Babu shakka ya yi mamakin ganinta, amma bai yi fushi ba. Sai ya miƙa kandarinsa na zinariya!—Esther 5:1, 2.

26. Me ya sa Kiristoci na gaskiya suke bukatar gaba gaɗi kamar na Esther, kuma me ya sa ba ta kammala aikin ba tukun?

26 Sarkin ya saurare ta. Esther ta kasance da aminci ga Jehobah kuma ta yi kasada da ranta don ta ceci ’yan’uwanta. Kiristoci na gaskiya a yau suna daraja irin wannan misalin. Yesu ya ce za a san da mabiyansa na gaskiya da halin sadaukar da kai. (Karanta Yohanna 13:34, 35.) Ana bukatar irin gaba gaɗin Esther don a yi hakan. Ko da yake Esther ta ɗauki mataki don ’yan’uwanta, amma ba ta kammala aikin ba tukun. Mene ne za ta ce don ta tabbatar wa sarkin cewa amininsa Haman, mugu maci amana ne? Me za ta yi don ta ceci ’yan’uwanta? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a babi na gaba.

^ sakin layi na 2 Xerxes na Ɗaya wanda mutane suka gaskata cewa shi ne Ahasuerus ya yi sarautar ƙasar Farisa a farkon ƙarni na biyar kafin zamanin Yesu.

^ sakin layi na 9 Ka duba akwatin nan ““Amsoshin Tambayoyi Game da Esther,” a Babi na 16.

^ sakin layi na 18 Wataƙila Haman ne Ba’amalak na ƙarshe tun da yake an halaka sauran tun zamanin Sarki Hezekiya.—1 Laba. 4:43.

^ sakin layi na 19 Haman ya ce zai ba da azurfa talanti 10,000, wanda a yau biliyoyin naira ne. Idan Ahasuerus ne Xerxes na Ɗaya, to kuɗin da Haman ya ce zai bayar ya sa sarkin farin ciki domin yana bukatar kuɗi sosai don ya yi yaƙi da ƙasar Girka.

^ sakin layi na 22 An san Xerxes na Ɗaya da mugun zafin rai. Wani ɗan tarihi mai suna Herodotus ya rubuta wasu abubuwa game da yaƙin da Xerxes ya yi da Girkawa. Sarkin ya ba da umurni cewa a gina gada ya ƙetare garin. Amma sa’ad da guguwa ta yi kaca-kaca da gadan, sai Xerxes ya ba da umurni a yanka mutanen da suka gina gadan. Ya kuma ce a bulale kogin yayin da yake karanta wani saƙo. Sa’ad da wani mawadaci ya roƙi Xerxes cewa ya sallami ɗansa daga zama soja, sarkin ya sa aka datsa yaron biyu kuma aka baza jikinsa don a yi wa wasu gargaɗi.