Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA BIYAR

Ku Komo “Wurin Makiyayi da Mai tsaron Rayukanku”

Ku Komo “Wurin Makiyayi da Mai tsaron Rayukanku”

Shin ka taɓa samun kanka kana fama da wasu ƙalubale da aka tattauna a cikin wannan ƙasidar? Idan haka ne, ba kai kaɗai ba ne. Amintattun bayin Jehobah Allah a dā da kuma a zamaninmu sun fuskanci irin waɗannan yanayin. Jehobah ya taimaka musu su sha kan waɗannan ƙalubalen, kuma zai taimaka maka kai ma.

Jehobah zai kasance tare da kai yayin da ka komo gare shi

KA TABBATA cewa Jehobah zai kasance tare da kai idan ka komo gare shi. Zai taimaka maka ka daina alhini da kuma ɓacin rai. Ƙari ga haka, za ka sami kwanciyar hankali don za ka kasance da lamiri mai kyau. Za ka sake yin marmarin bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwa masu bi. Yanayinka zai kasance kamar na wasu Kiristoci a ƙarni na farko da manzo Bulus ya ba wa wannan shawarar: “Dā kuna ɓacewa kamar tumaki; amma yanzu kun komo wurin Makiyayi da Mai tsaron rayukanku.”—1 Bitrus 2:25.

Babu abin da za ka yi da zai fi shawarar da ka yi na sake bauta wa Jehobah. Me ya sa? Don za ka faranta wa Jehobah rai. (Misalai 27:11) Kamar yadda ka sani, abubuwan da muke yi za su iya sa Jehobah baƙin ciki ko farin ciki, amma ba ya tilasta mana mu bauta masa. (Kubawar Shari’a 30:19, 20) Jehobah ya ba mu damar yin zaɓi, saboda haka, ba ya tilasta mana mu bauta masa. Idan muka bauta wa Jehobah da son rai da kuma ƙauna, muna nuna masa cewa mu masu aminci ne, kuma hakan yana faranta masa rai sosai. Hakika, ba abin da zai sa mu farin ciki kamar yin ibada ga wanda ya cancanci bautarmu, wato Jehobah.—Ayyukan Manzanni 20:35; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

Bugu da ƙari, idan ka soma bauta wa Jehobah kamar yadda ka yi a dā, za ka ƙarfafa dangantakarka da shi kuma za ka gamsu. (Matta 5:3) Ta yaya? Mutane a ko’ina suna so su san abin da ya sa muke raye. Suna neman amsoshi ga tambayoyi game da rayuwa. ’Yan Adam suna so su san amsoshin don Allah ya halicce su da wannan burin. Allah ya yi mu don mu bauta masa kuma mu ji daɗin rayuwa yayin da muke yin hakan. Babu abin da zai sa mu farin ciki kamar sanin cewa muna bauta wa Jehobah don muna ƙaunarsa.—Zabura 63:1-5.

Don Allah ka tuna cewa Jehobah yana so ka komo gare shi. Ta yaya za ka tabbata da hakan? Ka yi la’akari cewa kafin a shirya wannan ƙasidar, an natsu kuma an yi addu’a sosai. Wataƙila wani dattijo ko kuma wani ɗan’uwa ne ya ba ka ƙasidar. Hakan ya sa ka marmarin karantawa kuma ka ɗauki wasu matakai saboda shawarwarin da ke ciki. Hakan ya nuna cewa Jehobah bai yi watsi da kai ba. Akasin haka, yana jan hankalinka da sannu-sannu don ka sake bauta masa.—Yohanna 6:44.

Sanin cewa Jehobah bai manta da bayinsa da suka ɓace ba yana da ban ƙarfafa. Abin da wata ’yar’uwa mai suna Donna ta fahimta ke nan. Ta ce: “Da sannu a hankali na bar gaskiya, amma a wasu lokatai nakan yi tunani game da abin da aka rubuta a  Zabura 139:23, 24 cewa: ‘Ka yi bincikena, ya Ubangiji, ka san zuciyata: Ka auna ni, ka san tunanina: Ka duba ko da wata hanyar mugunta daga cikina, ka bishe ni cikin tafarki na har abada.’ Na san cewa ni ba na duniya ba ne kuma ban ji daɗin rayuwa ba sa’ad da na daina bauta wa Jehobah. Na san cewa ya kamata in kasance a cikin ƙungiyar Jehobah. Sai na soma fahimta cewa Jehobah bai yi watsi da ni ba; ni ne ke bukatar in komo gare shi. Abin da na yi ke nan kuma ina farin ciki cewa na yi hakan!”

“Sai na soma fahimta cewa Jehobah bai yi watsi da ni ba; ni ne ke bukatar in komo gare shi”

Muna fata cewa kai ma za ka sake samun “farin ciki na Ubangiji.” (Nehemiya 8:10) Ba za ka taɓa yin da-na-sani cewa ka komo ga Jehobah ba.