Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA HUƊU

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki

Yadda Za Ka Sa Rayuwar Iyalinka ta Zama Mai Farin Ciki
  • Menene ake bukata domin mutum ya zama mijin kirki?

  • Ta yaya mace za ta yi nasara wajen cika aikinta na matar aure?

  • Menene kasancewa iyayen kirki ya ƙunsa?

  • Ta yaya yara za su taimaka wajen sa rayuwar iyali ta zama mai farin ciki?

1. Menene zai sa rayuwar iyali ta zama mai farin cikin?

JEHOBAH ALLAH yana so rayuwar iyalinka ta kasance mai farin ciki. Kalmarsa Littafi Mai Tsarki ta ba da sharuɗa ga kowane mutum cikin iyali, ta kwatanta hakkin da Allah yake so kowa ya cika. Sa’ad da kowa ya sauƙe hakkinsa cikin jituwa da umurnan Allah, sakamakon suna gamsarwa. Yesu ya ce: “Gwamma dai waɗannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.”—Luka 11:28.

2. Farin ciki na iyali ya dangana ne bisa fahimtar menene?

2 Farin cikin iyali ya dangana bisa fahimtar Jehobah ne tushen iyali, shi ne kuma Yesu ya kira “Ubanmu.” (Matta 6:9) Dukan wata iyali a duniya ta kasance ne domin Ubanmu na sama—kuma hakika ya san abin da yake sa iyali farin ciki. (Afisawa 3:14, 15) To, menene Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da hakkin kowa cikin iyali?

ALLAH NE YA TSARA IYALI

3. Yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta farkon iyali, kuma ta yaya muka sani cewa hakan gaskiya ne?

3 Jehobah ya halicci mutane na farko, Adamu da Hauwa’u, ya haɗa su suka zama mata da miji. Ya saka su a cikin aljanna a duniya—gonar Adnin—kuma ya gaya musu su haifi ’ya’ya. “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya,” in ji Jehobah. (Farawa 1:26-28; 2:18, 21-24) Wannan ba labari ba ne ko kuma ƙage, domin Yesu ya nuna cewa abin da Farawa ta ce game da farkon iyali gaskiya ne. (Matta 19:4, 5) Ko da yake muna fuskantar matsaloli masu yawa a rayuwa, ba haka Allah ya nufa ba, bari mu ga yadda farin ciki zai iya kasancewa a cikin iyali.

4. (a) Ta yaya kowa cikin iyali zai iya taimaka wajen sa iyali farin ciki? (b) Me ya sa yin nazarin rayuwar Yesu yana da muhimmanci wajen sa iyali farin ciki?

4 Kowa cikin iyali zai iya sa rayuwar iyalin ta kasance mai farin ciki ta wajen yin koyi da Allah wajen nuna ƙauna. (Afisawa 5:1, 2) Amma, ta yaya za mu yi koyi da Allah, tun da ba ma iya ganin shi? Za mu iya koyo game da yadda Jehobah yake abubuwa domin ya aiko da Ɗansa na fari daga sama zuwa duniya. (Yohanna 1:14, 18) Sa’ad da yake duniya, wannan Ɗa, Yesu Kristi, ya yi koyi da Ubansa na samaniya sosai da ganinsa da saurarensa tamkar kasancewa da Jehobah ne da kuma saurarensa. (Yohanna 14:9) Saboda haka, koyo game da ƙauna da Yesu ya nuna da kuma yin koyi da misalinsa, kowannenmu zai iya taimaka wa wajen sa rayuwar iyali ta zama mai farin ciki.

MISALI GA MAZA

5, 6. (a) Ta yaya yadda Yesu ya bi da ikilisiya ya kafa misali ga maza? (b) Menene dole ne a yi domin a sami gafara daga zunubi?

5 Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata namiji ya bi da matarsa kamar yadda Yesu ya bi da almajiransa. Ka yi la’akari da wannan umurni na Littafi Mai Tsarki: ‘Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya bada kansa dominta; . . . Hakanan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna: gama babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyadda shi ya kan kiyaye shi, kamar yadda Kristi kuma ya kan yi da ikilisiya.’Afisawa 5:23, 25-29.

6 Ƙaunar Yesu ga ikilisiyar mabiyansa ya kafa misali mai kyau ga maza. Yesu “ya ƙaunace su har matuƙa,” ya sadaukar da ransa dominsu, ko da yake ba kamiltattu ba ne. (Yohanna 13:1; 15:13) Haka nan, aka aririci maza: ‘Ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.’ (Kolossiyawa 3:19) Menene zai taimaki namiji ya bi wannan gargaɗi, musamman ma a lokacin da matarsa ta yi kuskure? Ya kamata ya tuna da na shi kuskure da kuma abin da dole ne ya yi domin ya sami gafara daga Allah. Menene wannan? Dole ne ya gafarta wa waɗanda suka yi masa laifi kuma wannan ya haɗa da matarsa. Hakika, ita ma ya kamata ta yi haka nan. (Matta 6:12, 14, 15) Ka ga abin da ya sa wasu suka ce aure mai nasara, auren mutane ne biyu masu yin gafara?

7. Menene Yesu ya yi la’akari da shi, kuma wane misali ne ya kafa ga maza?

7 Ya kamata kuma maza su lura cewa a kullum Yesu yana nuna sanin ya kamata ga almajiransa. Yana yin la’akari da gazawarsu da kuma bukatunsu na zahiri. Alal misali, sa’ad da suka gaji, ya ce: “Ku zo da kanku waje ɗaya inda ba kowa, ku huta kaɗan.” (Markus 6:30-32) Mata ma suna bukatar a nuna musu sanin ya kamata. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su a matsayin waɗanda suka fi “rashin ƙarfi” kuma ya umurci maza su riƙa ba su “girma.” Me ya sa? Domin maza da mata “masu-tarayyan gado na alherin rai” ne. (1 Bitrus 3:7) Maza ya kamata su tuna cewa aminci, ba jinsi ba, ke sa mutum ya kasance da martaba a gaban Allah.—Zabura 101:6.

8. (a) Ta yaya ne namijin da ya ƙaunaci matarsa, “kansa ya ke ƙauna”? (b) Menene kasancewa “nama ɗaya” yake nufi ga mata da miji?

8 Littafi Mai Tsarki ya ce mijin da “ya ke ƙaunar matatasa kansa ya ke ƙauna.” Wannan haka yake domin mutum da matarsa ‘su ba biyu ba ne, amma nama ɗaya ne,’ kamar yadda Yesu ya nuna. (Matta 19:6) Saboda haka dole ne su tsaya wa juna a batun jima’i. (Misalai 5:15-21; Ibraniyawa 13:4) Za su iya yin haka idan suka nuna damuwa marar son kai ga bukatar juna. (1 Korinthiyawa 7:3-5) Abin lura ne wannan tunasarwa: ‘Babu mutum wanda ya taɓa ƙin jiki nasa; amma ya kan ciyadda shi ya kan kiyaye shi.’ Maza suna bukatar su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar kansu, suna kuma tuna cewa za su ba da lissafi ga nasu, shugaba, Yesu Kristi.—Afisawa 5:29; 1 Korantiyawa 11:3.

9. Wane hali ne na Yesu aka ambata a Filibbiyawa 1:8, kuma me ya sa ya kamata maza su nuna wannan hali ga matansu?

9 Manzo Bulus ya yi maganar “ƙaunar da Almasihu Yesu ke yi.” (Filibbiyawa 1:8 Littafi Mai Tsarki) Ƙaunar Yesu hali ne mai daɗaɗawa, wadda mata da suka zama almajiransa suke so. (Yohanna 20:1, 11-13, 16) Dukan mata suna bukatar ƙaunar mazansu.

MISALI GA MATA

10. Ta yaya Yesu ya ba da misali ga mata?

10 Iyali ƙungiya ce, kuma domin ta yi tafiya daidai, tana bukatar shugaba. Yesu ma yana da Shugaban da yake miƙa wa kai. “Kan Kristi kuma Allah ne,” yadda “kan mace kuma namiji ne.” (1 Korinthiyawa 11:3) Yadda Yesu yake miƙa wa Shugabancin Allah kai misali ne mai kyau, tun da dukanmu muna da shugaban da muke miƙa wa kai.

11. Wane irin hali ya kama mata ta nuna wa mijinta, kuma menene zai kasance sakamakon halinta?

11 Mutane ajizai suna yin kuskure kuma sau da yawa suna gaza kasance shugabannin iyali da suka dace. Saboda haka, menene mace ya kamata ta yi? Kada ta raina abin da mijinta ya yi, ko kuma ta yi ƙoƙarin ƙwace shugabancinsa. Ya kamata mace ta tuna cewa a idanun Allah, tawali’u da natsuwa, waɗannan abubuwa ne masu martaba a gun Allah. (1 Bitrus 3:4) Ta wajen nuna irin wannan hali, zai kasance da sauƙi a gare ta ta miƙa kai irin na ibada, har a lokaci masu wuya. Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:33) Amma idan bai karɓi Yesu a zaman Shugabansa ba fa? Littafi Mai Tsarki ya aririci mata: ‘Ku yi zaman biyayya ga mazaje naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.’1 Bitrus 3:1, 2.

12. Me ya sa ba laifi ba ne mace ta faɗi ra’ayinta cikin ladabi?

12 Ko mijin mai bi ne ko a’a, ba raini ba ne mace ta faɗi ra’ayinta da ya bambanta da na shi cikin ladabi. Ra’ayinta zai iya kasance daidai, kuma dukan iyalin za su amfana idan ya saurare ta. Ko da yake Ibrahim bai yarda da ra’ayin matarsa Saratu ba sa’ad da ta ba da shawarar abin da za a yi a magance wata matsala na iyali, Allah ya gaya masa: “Ka ji maganarta.” (Farawa 21:9-12) Hakika, sa’ad da mijin ya yanke shawarar da ba ta saɓa wa dokar Allah ba, matarsa za ta nuna miƙa kanta ta wajen taimaka masa.—Ayukan Manzanni 5:29; Afisawa 5:24.

Wane misali ce mai kyau Saratu ta kafa wa matan aure?

13. (a) Menene Titus 2:4, 5 suka aririci matan aure su yi? (b) Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da rabuwa da kuma kisan aure?

13 A wajen cika aikin ta, mace tana iya yin abubuwa da yawa domin ta kula da iyalinta. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa matan aure su “yi ƙaunar mazajensu, su yi ƙaunar ’ya’yansu, su zama masu-hankali, masu-tsabtan rai, masu-aiki a gidajensu, masu-nasiha, masu-biyayya ga mazajensu.” (Titus 2:4, 5) Matar da ta yi irin wannan za a ƙaunace ta kuma za a daraja ta a iyalinta. (Misalai 31:10, 28) Tun da aure gamin mutane ne biyu ajizai, yanayi mai wuya ƙwarai zai iya kai wa ga rabuwa ko kuma kashe aure. Littafi Mai Tsarki ya yarda a rabu domin wani yanayi. Duk da haka, kada a ɗauki rabuwa da wasa, domin Littafi Mai Tsarki ya yi gargaɗi: “Kada matan ta rabu da mijinta . . . , mijin kuma kada shi rabu da matatasa.” (1 Korinthiyawa 7:10, 11) Zina ne kawai daga ɗaya cikin ma’auratan, zai iya ba da damar kashe aure bisa ga Nassosi.—Matta 19:9.

MISALI MAI KYAU GA IYAYE

14. Yaya Yesu ya bi da yara, kuma menene yara suke bukata daga iyayensu?

14 Yesu ya kafa misali mai kyau ga iyaye a hanyar da ya bi da yara. Sa’ad da wasu suke so su hana waɗannan yara ƙanana zuwa wurin Yesu, ya ce: “Ku bar yara ƙanƙanana su zo gareni; kada ku hana su.” Littafi Mai Tsarki ya ce sai “ya rungume su, ya sa musu albarka, ya ɗibiya musu hannuwa.” (Markus 10:13-16) Tun da Yesu ya ba da lokaci ga yara ƙanana, bai kamata mu ma mu yi haka ba ga yaranmu maza da mata? Suna bukatar, ba ɗan lokaci ba, amma lokaci mai yawa. Kuna bukatar ku ɗauki lokaci domin ku koyar da su, domin wannan shi ne abin da Jehobah ya umurci iyaye su yi.—Kubawar Shari’a 6:4-9.

15. Menene iyaye za su yi domin su kāre ’ya’yansu?

15 Sa’ad da wannan duniyar ta ci gaba da zama muguwa, yara suna bukatar iyaye da za su kāre su daga mutanen da za su nemi su yi musu lahani, irinsu masu lalata da yara. Ka yi la’akari da yadda Yesu ya kāre almajiransa, waɗanda ya kira cikin ƙauna “ ’ya’ya ƙanƙanana.” Sa’ad da aka kama shi kuma za a kashe shi ba da daɗewa ba, Yesu ya yi musu hanyar tsira. (Yohanna 13:33; 18:7-9) Iyaye, kuna bukatar ku kasance a faɗake domin ƙoƙarin Iblis ya yi wa ’ya’yanku ƙanƙanana lahani. Kuna bukatar ku yi musu gargaɗi a kan lokaci. * (1 Bitrus 5:8) Yanzu sun fi fuskantar haɗari ta zahiri, ta ruhaniya, da kuma ta ɗabi’a.

Menene iyaye za su iya koya daga yadda Yesu ya bi da yara?

16. Menene iyaye za su iya koya daga hanyar da Yesu ya bi da ajizancin almajiransa?

16 A daren da Yesu zai mutu, almajiransa sun yi gardama game da wanda ya fi girma a tsakaninsu. Maimakon ya yi fushi da su, Yesu ya ci gaba da koyar da su da kalmomi da kuma misali. (Luka 22:24-27; Yohanna 13:3-8) Idan kana da ’ya’ya, ka ga yadda za ka iya bin misalin Yesu a wannan hanyar wajen koyar da yaranka? Hakika, suna bukatar horo, amma ya kamata a yi shi ‘da adalci’ ba cikin fushi ba. Ba za ka so ka yi maganganun rashin tunani “kamar sussukan takobi.” (Irmiya 30:11; Misalai 12:18) Horo ya kamata a yi shi a hanyar da yaro daga baya zai fahimci cewa hakan daidai ne.—Afisawa 6:4; Ibraniyawa 12:9-11.

MISALI GA YARA

17. A wace hanya ce Yesu ya kafa misali mai kyau ga yara?

17 Akwai abin da yara za su koya kuwa daga Yesu? Hakika kuwa! Ta wajen misalinsa, Yesu ya nuna yadda ya kamata yara su yi wa iyayensu biyayya. “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mini,” in ji shi. Ya daɗa cewa: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:28, 29) Yesu yana biyayya ga Ubansa na samaniya, kuma Littafi Mai Tsarki ya gaya wa yara su yi biyayya ga iyayensu. (Afisawa 6:1-3) Ko da yake Yesu yaro ne kamili, ya yi wa iyayensa, Yusufu da Maryamu, da suke ajizai biyayya. Wannan hakika, ya sa kowa a cikin iyalin Yesu ya yi farin ciki!—Luka 2:4, 5, 51, 52.

18. Me ya sa ko da yaushe Yesu yana yi wa Ubansa na samaniya biyayya, kuma waye yake yin farin ciki sa’ad da yara suka yi wa iyayensu biyayya?

18 A waɗanne hanyoyi ne yara za su iya zama kamar Yesu kuma su sa iyayensu su yi farin ciki? Hakika, a wasu lokatai zai yi wa yara wuya su yi wa iyayensu biyayya, amma Allah yana so yara su yi wa iyayensu biyayya. (Misalai 1:8; 6:20) Koyaushe Yesu yana yi wa Ubansa na samaniya biyayya, har ma a lokaci mai wuya. Akwai lokacin da nufin Allah ne Yesu ya yi wani abin da yake da wuya sosai, Yesu ya ce: “Ka kawar mini da wannan ƙoƙon [wani abin da ake bukata a gare shi].” Duk da haka, Yesu ya yi abin da Allah ya ce masa, domin ya fahimci cewa Ubansa ya san abin da ke mai kyau. (Luka 22:42) Idan suka koyi su yi biyayya, yara za su sa iyayensu da kuma Ubansu na samaniya su yi farin ciki ƙwarai. *Misalai 23:22-25.

Menene ya kamata yara su tuna sa’ad da aka jarrabe su?

19. (a) Ta yaya Shaiɗan yake jarabtar yara? (b) Yaya lalata na yara zai shafi iyayensu?

19 Shaiɗan ya jarrabi Yesu, kuma za mu iya tabbata cewa zai jarrabi yara su yi abin da ba shi da kyau. (Matta 4:1-10) Shaiɗan Iblis yana amfani da matsi na tsara, wanda yake da wuya a tsayayya wa. Yana da muhimmanci ƙwarai kada yara su yi abota da masu yin abin da ba shi da kyau! (1 Korinthiyawa 15:33) ’Yar Yakubu Dinatu ta yi abota da mutane da ba sa bauta wa Jehobah, kuma haka ya saka ta cikin masifa. (Farawa 34:1, 2) Ka yi tunanin yadda zai shafi iyalinka idan wani cikin iyalin ya faɗa cikin lalata!—Misalai 17:21, 25.

ABIN DA ZAI SA IYALI FARIN CIKI

20. Domin a more rayuwar iyali, menene dole waɗanda suke cikin iyali za su yi?

20 Za a iya magance matsala a iyali idan aka yi amfani da gargaɗin Littafi Mai Tsarki. Hakika, amfani da wannan gargaɗi zai sa iyali farin ciki. Saboda haka, maza, ku ƙaunaci matanku, kuma ku bi da su kamar yadda Yesu yake bi da ikilisiyarsa. Mata, ku miƙa kai ga shugabancin mazanku, kuma ku bi misalin macen kirki da aka kwatanta a Misalai 31:10-31. Iyaye, ku koyar da ’ya’yanku. (Misalai 22:6) Ubanni, ku sarrafa iyalanku da kyau. (1 Timothawus 3:4, 5; 5:8; Kolossiyawa 3:20) Kuma yara, ku yi biyayya ga iyayenku. Babu wanda yake cikin iyali da yake kamili, domin ba wanda ba ya kuskure. Saboda haka, ku kasance da tawali’u, kuna neman gafarar juna.

21. Wane bege ne mai ban sha’awa muke jira, kuma ta yaya za mu more farin ciki na rayuwar iyali a yanzu?

21 Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi gargaɗi da umurni masu muhimmanci domin rayuwar iyali. Bugu da ƙari, ya koya mana game da sabuwar duniya ta Allah da kuma aljanna ta duniya wadda za ta cika da mutane masu farin ciki waɗanda suke bauta wa Jehobah. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Wannan bege ne mai ban sha’awa! Har a yanzu, za mu iya more farin ciki na iyali ta wajen amfani da umurnin Allah da suke cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki.

^ sakin layi na 15 Za a sami taimako game da yadda za a kāre yara a babi na 32 na littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

^ sakin layi na 18 Idan iyayen suka ce wa yaro ya ƙeta dokar Allah, a nan kawai yaro zai iya yin rashin biyayya.—Ayukan Manzanni 5:29.