Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Wata ’yar’uwa mai wa’azi na cikakken lokaci tana bishara a Koriya, a 1931; dama: Yin wa’azi a yaren kurame a Koriya a yau

SASHE NA 2

Wa’azin Mulkin​—Yaɗa Bishara a Dukan Duniya

Wa’azin Mulkin​—Yaɗa Bishara a Dukan Duniya

KA YI shirin fita wa’azi a safiyar ranar da ka sami hutu daga wajen aiki. Ka ɗan yi jinkirin fita saboda gajiya kuma kana jin cewa zai dace ka ɗan huta! Amma sai ka yi addu’a game da batun kuma ka fita wa’azi. A ranar ka fita wa’azi ne tare da wata tsohuwar ’yar’uwa mai aminci wadda jimiri da alherinta sun taɓa zuciyarka sosai. Yayin da kuke bi gida-gida kuna wa’azin Mulkin, sai ka tuna cewa ’yan’uwa maza da mata a faɗin duniya ma suna yin hakan kuma suna yin amfani da irin littattafan da kuke amfani da su. Ƙari ga haka, duk kuna amfana ne daga koyarwa iri ɗaya. Sa’ad da ka koma gida, ka ji wani irin sabon ƙarfi kuma ka yi murnar cewa ba ka zauna a gida ba!

A yanzu haka, wa’azin bishara shi ne aiki mafi muhimmanci na Mulkin Allah. Yesu ya annabta cewa za a yi aikin wa’azin nan a faɗin duniya a wannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 24:14) Ta yaya annabcin nan yake cika? A wannan sashen, za mu tattauna game da mutanen da suke wa’azin Mulkin da tsarin da suke bi da kuma kayan aikin da suke amfani da shi da ke taimaka wa miliyoyin mutane a faɗin duniya su ga cewa Mulkin Allah abu ne na gaskiya.

A WANNAN SASHEN

BABI NA 6

Masu Wa’azi​—Masu Wa’azi Sun Ba da Kansu da Yardan Rai

Me ya sa Yesu ya kasance da tabbaci cewa zai sami mutanen da za su yi wa’azi da yardan rai a kwanaki na ƙarshe? Ta yaya za ka nuna cewa kana biɗan Mulkin farko a rayuwarka?

BABI NA 7

Hanyoyin Yin Wa’azi​—Yin Amfani da Hanyoyi Dabam-dabam don Yin Wa’azi

Ka koya hanyoyi dabam-dabam da bayin Allah suka yi amfani da su don yaɗa bishara ga jama’a kafin ƙarshe ya zo.

BABI NA 8

Kayan Aiki don Yin Wa’azi​—⁠Wallafa Littattafai Domin Mutane a Faɗin Duniya

Ta yaya aikin fassara da muke yi ya nuna cewa muna da goyon bayan Yesu? Waɗanne abubuwa game da littattafanmu ne suka tabbatar maka cewa Mulkin na gaskiya ne?

BABI NA 9

Sakamakon Yin Wa’azi​—‘Gonaki Sun Nuna Sun Isa Girbi’

Yesu ya koya wa almajiransa muhimman darussa guda biyu game da wannan aikin girbi mai girma. Ta yaya waɗannan darussan suke shafarmu a yau?