Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba

Yadda Rayuwa Za Ta Kasance a Nan Gaba

Ka taɓa tunanin yadda rayuwa za ta kasance a nan gaba? Littafi Mai Tsarki ya nuna muhimman abubuwan da za su faru da za su shafi dukan mutane.

Yesu ya bayyana yadda za mu gane cewa “Mulkin Allah ya yi kusa.” (Luka 21:31) Ya annabta cewa, wasu daga cikin abubuwan da za su faru su ne, za a yi yaƙe-yaƙe, da girgizar ƙasa, da matsananciyar yunwa, kuma cututtuka za su bazu. Abubuwan da muke gani a yau ke nan, ko ba haka ba?​—Luka 21:​10-17.

Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a “kwanakin ƙarshe,” halayen mutane za su daɗa muni. Za ka iya karanta yadda aka kwatanta hakan a 2 Timoti 3:​1-5. Idan ka yi la’akari da halayen mutane da kuma abubuwan da suke faruwa a yau, ba shakka za ka yarda cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ne yake cika.

Me hakan yake nufi? Lokaci ya kusa da Mulkin Allah zai gyara duniya. (Luka 21:36) A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya yi alkawari cewa zai gyara dukan abubuwan da suka lalace a duniya, kuma zai albarkaci bayinsa da suke duniya. Ga wasu daga cikin albarkun da za su samu.

GWAMNATI MAI ADALCI

“Aka kuwa ba shi [Yesu] sarauta, da ɗaukaka da mulki, domin dukan ƙabilu, da al’ummai, da yare dabam-dabam su [“yi masa hidima,” NW]. Sarautarsa ta har abada ce, mulki ne wanda ba zai ƙare ba. Mulkinsa ba za a taɓa halakar da shi ba.”​DANIYEL 7:14.

Yadda za ka amfana: Za ka ji daɗin rayuwa a ƙarƙashin gwamnatin Allah wadda za ta yi sarauta bisa dukan duniya. Kuma Yesu ne Sarkin.

ƘOSHIN LAFIYA

“Ba mazaunin ƙasar da zai ce, ‘Ina ciwo.’”​ISHAYA 33:24.

Yadda za ka amfana: Ba za ka ƙara yin rashin lafiya ko ka zama mai naƙasa ba kuma za ka rayu har abada.

CIKAKKIYAR SALAMA

‘Zai tsai da yaƙe-yaƙe a dukan duniya.’​ZABURA 46:9.

Yadda za ka amfana: Ba za ka ƙara jin tsoro cewa za a yi yaƙi ba, balle a ce mutane za su wahala saboda yaƙi.

DUNIYA ZA TA CIKA DA MUTANEN KIRKI

“Mugaye za su [“shuɗe,” NW ] . . . amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar.”​ZABURA 37:​10, 11.

Yadda za ka amfana: Mugaye ba za su kasance a duniya a lokacin ba, mutanen da suke yi wa Allah biyayya ne kaɗai za su kasance.

DUNIYA ZA TA ZAMA ALJANNA

“Za su gina gidaje, su zauna a cikinsu, za su shuka gonakin inabi, su ci amfaninsu.”​ISHAYA 65:​21, 22.

Yadda za ka amfana: Duniya gaba ɗaya za ta yi kyau sosai. Allah zai amsa addu’ar da muke yi cewa a yi nufinsa “a cikin duniya.”​—Matiyu 6:10.