Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yaya Allah Yake Ji Game da Wahalar da Kake Sha?

Yaya Allah Yake Ji Game da Wahalar da Kake Sha?

Wasu mutane sun yi imani cewa Allah ba ya ganin wahalar da muke sha kuma bai damu da hakan ba.

KA GA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

  • Allah yana gani kuma ya damu

    “Yahweh kuwa ya lura cewa muguntar ’yan Adam ta yi yawa a duniya, . . .  kuma zuciyarsa ta ɓaci ƙwarai.”​—Farawa 6:​5, 6.

  • Allah zai cire dukan wahalar da muke sha

    “Ba da daɗewa ba mugaye za su ɓace, ko ka duba inda suke a dā, ba za ka gan su ba. Amma masu sauƙin kai za su gāji ƙasar, su sami farin cikinsu cikin salama a yalwace.”​—Zabura 37:​10, 11.

  • Abin da Allah yake so ya yi maka

    ‘Na san irin shirin da nake da shi domin ku. Shiri ne na alheri, ba na masifa ba, domin in ba ku bege da rayuwa ta nan gaba. Ni Yahweh na faɗa. Sa’an nan za ku yi kira gare ni, ku juyo, ku yi addu’a gare ni, ni zan kuwa ji ku.’​—Irmiya 29:​11, 12.

    “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.”​—Yaƙub 4:8.