Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin ’yan Adam ne suka tsara addini?

WASU SUN YI IMANI CEWA addini abu ne da ’yan Adam suka tsara. Wasu kuma suna gani cewa Allah yana amfani da addini ne don ya sa mu kusace shi. Mene ne ra’ayinka?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

Akwai “addini mai-tsarki marar-ɓāci a gaban Allah Ubanmu.” (Yaƙub 1:27) Allah ne ya tsara addini mai-tsarki marar aibi.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Addinin da ke faranta wa Allah rai yana koyar da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. —Yohanna 4:23, 24.

  • Allah ba ya son addinin da ke koyar da ra’ayin ’yan Adam.—Markus 7:7, 8.

Wajibi ne mu kasance da addini?

ME ZA KA CE?

  • E

  • A’a

  • Ya dangana ga yanayin

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu.” (Ibraniyawa 10:24, 25) Allah yana so bayinsa su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

ME KUMA ZA MU IYA KOYA DAGA LITTAFI MAI TSARKI?

  • Wajibi ne bayin Allah su kasance da imani ɗaya.—1 Korintiyawa 1:10, 11.

  • Dukan mutanen da ke bin addinin da Allah ya amince da shi ʼyanʼuwa ne.—1 Bitrus 2:17.