Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Sani?

Ka Sani?

Bulo da aka tono a Babila ta dā da kuma yadda aka yi su sun nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne

MASU tonan ƙasa sun gano miliyoyin bulo, waɗanda aka gina Babila da su. Wani mai tonan ƙasa mai suna Robert Koldewey, ya ce idan za a gasa irin wannan bulon, akan je “bayan gari ne a shirya wurin gashi inda za a sami laka mai kyau da kuma isashen itacen da za a yi amfani da su.”

Masu tonan ƙasa sun ga abin da ya nuna cewa hukumomin gwamnati na Babila suna amfani da wurin gasa bulo ɗin su yi mugayen abubuwa. Akwai wani farfesa mai suna Paul-Alain Beaulieu, wanda masanin tarihi da kuma yaren Assuriya ta dā ne. Farfesan ya ce: “Rubuce-rubuce da yawa na Babiloniyawa . . . sun nuna yadda sarkinsu ya ba da umurni cewa a saka waɗanda suka yi masa rashin biyayya ko kuma suka rena abubuwa masu tsarki a cikin wurin da ake gasa bulon don su ƙone a wurin.” Alal misali, wani rubutu da aka yi a zamanin Sarki Nebukadnezzar ya ce: “Ku halaka su, ku ƙona su, ku gasa su . . . a wurin gashin nan, . . . ku sa hayaƙinsu ya tashi sama, ku kashe su ta wurin jefa su cikin wutar.”

Wannan yana tuna wa masu karanta Littafi Mai Tsarki abin da ya faru a Littafin Daniyel sura 3. Surar ta ce Sarki Nebukadnezzar ya gina babban gunki na zinariya a filin Dura da ke bayan garin Babila. Saꞌad da wasu matasa Ibraniyawa guda uku, wato Shadrak, da Meshak, da Abednego suka ƙi su yi wa gunkin sujada, Sarki Nebukadnezzar ya yi fushi sosai. Sai ya ba da umurni cewa a “ƙara zuga wuta a gidan wuta har ta yi zafi sau bakwai fiye da yadda aka yi a dā,” kuma ya sa aka “jefa su cikin wutar.” Wani malaꞌika mai iko sosai ne ya ceto su daga cikin wutar.​—Dan. 3:​1-6, 19-28.

© The Trustees of the British Museum. Licensed under CC BY-NC-SA 4.0. Source

Wani bulo da aka gasa ɗauke da sunan Nebukadnezzar

Bulon da aka tono daga Babila ta dā ma sun nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa gaskiya ne. Wasu daga cikin bulon suna ɗauke da rubuce-rubuce da ke yabon sarkin Babila. Ɗaya daga cikin rubuce-rubucen ya ce: “Nebukadnezzar, Sarkin Babila . . . Ga fada da Ni Sarki Mai Girma na gina . . . Bari jikokina su yi mulki a cikinta har abada.” Wannan rubutun ya yi kama da abin da ke Daniyel 4:30. A ayar, Sarki Nebukadnezzar ya buga ƙirji yana cewa: “Ashe, ba wannan ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina da ƙarfin ikona ba? Ba ni ne na gina ta domin ta zama gidan mulkina ba? Ba ni na gina ta domin darajar ɗaukakata ba?”