Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wannan Wurin Ne Muke Bauta

Wannan Wurin Ne Muke Bauta

“Himma domin gidanka za ta cinye ni.”—YOH. 2:17.

WAƘOƘI: 127, 118

1, 2. (a) Waɗanne wuraren ibada ne bayin Jehobah suka yi amfani da shi a dā? (b) Yaya Yesu ya ɗauki haikalin Allah da ke Urushalima? (c) Don wane dalili ne aka rubuta wannan talifin?

TUN zamanin dā, bayin Allah suna da wuraren da aka tsara don yin ibada. Mai yiwuwa, Habila ya yi amfani da bagadi don ya ba da hadayu ga Allah. (Far. 4:3, 4) Nuhu da Ibrahim da Ishaƙu da Yakubu da kuma Musa sun gina bagadai. (Far. 8:20; 12:7; 26:25; 35:1; Fit. 17:15) Jehobah ya ba Isra’ilawa umurni su gina mazauni. (Fit. 25:8) Daga baya sun gina haikali don su riƙa bauta wa Jehobah. (1 Sar. 8:27, 29) Bayan da Yahudawa suka dawo daga bauta a Babila, suna yin taro a kai a kai a majami’u. (Mar. 6:2; Yoh. 18:20; A. M. 15:21) Kiristoci a ƙarni na farko sun yi taro a gidajen Kiristoci ’yan’uwansu. (A. M. 12:12; 1 Kor. 16:19) A yau, mutanen Jehobah suna yin taro don ibada da kuma ilimantarwa a cikin Majami’un Mulki da yawa a faɗin duniya.

2 Saboda yadda Yesu yake son yin bauta a haikalin Jehobah da ke Urushalima, almajiransa su tuna abin da marubucin zabura ya fada cewa: “Himma domin gidanka ya cika zuciyata.” (Zab. 69:9; Yoh. 2:17) Ko da yake ba Majami’ar Mulki da za a kira “gidan Ubangiji” kamar yadda aka kira haikali da ke Urushalima. (2 Laba. 5:13; 33:4) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da suka nuna yadda ya kamata mu riƙa amfani da Majami’ar Mulki da kuma daraja ta. Za a tattauna wasu ƙa’idodin a cikin wannan talifin. Ƙari ga haka, za mu bincika yadda ƙa’idodin nan za su taimaka mana mu daraja Majami’un Mulki da kula da su da kuma yadda za mu riƙa ba da gudummawa don gina Majami’un Mulki. *

MU RIƘA DARAJA TARONMU

3-5. Mene ne ake yi a cikin Majami’ar Mulki, kuma yaya hakan ya kamata ya shafi yadda muke ɗaukan taronmu?

3 Majami’ar Mulki ce ainihin wurin da mutane suke yin taro don su bauta wa Jehobah. Taron da ake yi a Majami’ar Mulki a kowane mako yana cikin abubuwa da Jehobah yake tanadarwa don mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. A wurin ne muke samun ƙarfafa da kuma ja-gora daga ƙungiyarsa. Hakan yana nufin cewa Jehobah da Ɗansa ne suke gayyatar dukan waɗanda suke halartan taro. Duk da cewa ana gayyatar mu zuwa taro kowane mako don mu “ci daga table na Ubangiji,” wato don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, bai kamata mu yi wasa da wannan gayyatar ba.—1 Kor. 10:21.

4 Jehobah yana so mu riƙa taro don yin ibada da kuma ƙarfafa juna. Ta wurin ja-gorar ruhu mai tsarki, Jehobah ya sa manzo Bulus ya umurce mu kada mu fasa zuwa taro. (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Idan muna daraja Jehobah ba za mu fasa taro ba sai dai ya zama dole. Muna nuna cewa muna godiya ga Jehobah da kuma tanadin da ya yi ta wajen yin shiri don taro da dukan zuciyarmu da kuma ta yin kalami.—Zab. 22:22.

5 Ya kamata halinmu a taro ya nuna cewa muna daraja Majami’ar Mulki da kuma ayyuka na ibada da ake yi a wajen. Ya dace halinmu ya ɗaukaka sunan Jehobah, da yake ana ganin wannan sunan a allon da ke ɗauke da sunan Majami’ar Mulki.—Gwada da 1 Sarakuna 8:17.

6. Mene ne wasu mutane suka ce game da Majami’un Mulki da waɗanda suke halartan taro a wajen? (Ka duba hoton da ke shafi na 27.)

6 Mutane suna lura da yadda muke daraja Majami’un Mulki. Alal misali, wani mutum a Turkiya ya ce: “Na lura cewa Majami’ar Mulki tana da tsabta da kuma tsari, kuma hakan ya burge ni. Mutanen sun yi shiga mai kyau, suna murmushi kuma sun gai da ni da fara’a. Hakan ya burge ni sosai.” Mutumin ya soma halartan taro a kai a kai kuma ya yi baftisma ba da daɗewa bayan hakan. A wani birni a ƙasar Indonisiya, ’yan’uwa sun gayyaci ma’aikatan gwamnati da kuma maƙwabta don su zagaya sabuwar Majami’ar Mulki a lokacin da suke son su keɓe ta ga Jehobah. Magajin garin ya halarta. Ingancin ginin da yadda aka tsara shi da kuma kyakkyawan lambu da ke ciki sun burge shi. Ya ce: “Tsabtar majami’ar ta nuna cewa ku masu bi ne da gaske.”

Halinmu zai iya nuna cewa ba ma daraja Allah (Ka duba sakin layi na 7 da 8)

7, 8. Waɗanne batutuwa masu muhimmanci ne ya kamata mu riƙa la’akari da su sa’ad da muka halarci taro?

7 Ya kamata a ga cewa muna daraja Allahn da ya gayyace mu zuwa taron Kirista ta wajen halinmu da shigar da muke yi da kuma adonmu mai kyau. Ƙari ga haka, bai kamata mu riƙa yin abubuwa da suka wuce gona da iri ba. An lura cewa wasu suna da taurin ra’ayi game da halin da ya dace a taron ikilisiya, kuma wasu suna sake jiki ainun a Majami’ar Mulki kamar a gida suke. Hakika Jehobah yana son bayinsa da kuma baƙi su saki jiki a Majami’ar Mulki. Amma, bai kamata waɗanda suka halarci taro su yi shigar da ba ta dace ba ko su riƙa aika saƙo ta wayar salula ko su riƙa surutu ko kuma su riƙa cin abinci da sauransu a lokacin da ake taro. Ya kamata iyaye su horar da yaransu su fahimci cewa Majami’ar Mulki ba wurin yin gudu ko kuma wasa ba.—M. Wa. 3:1.

8 Yesu ya yi fushi sa’ad da ya ga cewa mutane suna sayar da abubuwa a haikalin Allah, kuma ya kore su. (Yoh. 2:13-17) Muna bauta wa Jehobah da kuma koya game da shi a Majami’un Mulki. Saboda haka, ba zai dace ba mu yi ma’amala da ba ta shafi bautarmu ba a wajen.—Gwada da Nehemiya 13:7, 8.

MUNA BA DA GUDUMMAWA DA KUMA GINA MAJAMI’UN MULKI

9, 10. (a) Ta yaya ake ba da gudummawa da gina sababbin Majami’un Mulki, kuma mene ne sakamakon hakan? (b) Ta yaya aka taimaka wa ikilisiyoyi da ba su da isashen kuɗin gina Majami’ar Mulki?

9 Ƙungiyar Jehobah tana iya ƙoƙarinta don ta gina Majami’un Mulki madaidaici. Mutane suna ba da kansu don tsara yadda za a gina da kuma gyara Majami’un Mulki, kuma suna yin hakan kyauta. Mene ne sakamakon? Tun daga ranar 1 ga Nuwamba, shekara ta 1999, an gina kyawawan wuraren bauta ta gaskiya fiye da 28,000 a faɗin duniya. Hakan yana nufin cewa a cikin shekaru 15 da suka shige, an gina Majami’un Mulki kimanin biyar a kowace rana.

10 Ƙungiyar Jehobah tana ƙoƙari ta tallafa wa gine-ginen Majami’un Mulki a duk wuraren da ake bukatar yin hakan. Ana yin hakan bisa ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da ta ce waɗanda suke da yalwa su taimaka wa waɗanda ba su da shi domin “daidaita ta kasance.” (Karanta 2 Korintiyawa 8:13-15.) Saboda haka, an gina sababbin Majami’un Mulki wa ikilisiyoyin da ba su da isashen kuɗin ginawa.

11. Mene ne wasu ’yan’uwa suka ce game da sabuwar Majami’ar Mulki da aka gina musu, kuma yaya hakan yake sa ka ji?

11 Wasu ’yan’uwa a ikilisiya da ke Costa Rica da suka amfana daga wannan tanadin ta rubuta cewa: “Muna ji kamar muna mafarki ne sa’ad da muka tsaya a gaban Majami’ar Mulki! Hakan ya ba mu mamaki. Majami’ar tana da kyaun gaske kuma an gama kome da kome game da ginin a cikin kwanaki takwas kawai! Hakan ya yiwu don taimakon Jehobah da tsarin ƙungiyarsa take bi da kuma taimakon ’yan’uwanmu. Hakika, wannan wurin ibada kyauta ce mai tamani da Jehobah ya ba mu. Muna farin ciki matuƙa don samun wannan majami’ar.” Jin irin wannan furuci na godiya game da sababbin Majami’un Mulki suna sa mu farin ciki, kuma mun san cewa ’yan’uwanmu da ke wurare dabam-dabam a faɗin duniya suna farin ciki. A bayyane yake cewa Jehobah yana albarkar aikin gine-ginen Majami’un Mulki, domin da zarar an gama, sai mutane su cika Majami’un don su ƙara sanin Mahaliccinmu mai ƙauna.—Zab. 127:1.

12. Ta yaya za ka iya taimakawa a gine-ginen Majami’un Mulki?

12 ’Yan’uwa da yawa sun yi farin ciki sosai da yake sun taimaka wajen gina Majami’ar Mulki. Ko da za mu iya saka hannu a gine-ginen ko a’a, dukan mu muna iya taimakawa ta ba da gudummawarmu. Idan muka yi hakan, muna bin misalin mutane da ke zamanin dā da suka yin ɗokin ba da gudummawa don gina wuraren bauta saboda hakan yana ɗaukaka Jehobah.—Fit. 25:2; 2 Kor. 9:7.

MU RIƘA TSABTACE MAJAMI’AR MULKI

13, 14. Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa tsabtace da kuma shirya Majami’ar Mulki yana da muhimmanci?

13 Muddin an gina sabuwar Majami’ar Mulki, muna bukatar mu riƙa tsabtace da kuma shirya ta da kyau da yake Allah da muke bauta wa, mai tsari ne. (Karanta 1 Korintiyawa 14:33, 40.) Don mu zama masu tsabta da tsarki kamar Jehobah, wajibi ne mu kasance da tsarki a bautarmu da tunaninmu da ayyukanmu. Ƙari ga haka, muna bukatar mu tsabtace jikinmu.—R. Yoh. 19:8.

14 Idan muka tsabtace da kuma shirya Majami’ar Mulkin da kyau, hakan zai sa mu yi marmarin gayyatar mutane zuwa taronmu. Ƙari ga haka, mutane za su ga cewa wa’azin da muke yi game da sabuwar duniya gaskiya ne. Za su ga cewa muna bauta wa Allah mai tsarki kuma ba da daɗewa ba zai mai da wannan duniyar aljanna.—Isha. 6:1-3; R. Yoh. 11:18.

15, 16. (a) Me ya sa tsabtace Majami’ar Mulki bai da sauƙi, amma me ya sa yin hakan yake da muhimmanci? (b) Wane tsari ne kuke bi don tsabtace Majami’ar Mulki, kuma wane gata ne kowannenmu yake da shi?

15 Wasu ’yan’uwa sukan ɗauki tsabtace Majami’ar Mulki da muhimmanci fiye da wasu. Mai yiwuwa abubuwan da ke shafan ra’ayinsu sun ƙunshi yadda aka yi renonsu, kuma wasu suna zama a wuri mai ƙura ko kuma inda hanyoyin ba su da kyau ko wuri mai taɓo. Ƙari ga haka, wataƙila ba su da isashen ruwa da kuma kayan shara. Ko da wane ra’ayi ne ’yan’uwa suke da shi da kuma yanayinsu, ya kamata mu tsabtace da kuma shirya Majami’ar Mulki da kyau, tun da yake a wurin ne muke bauta wa Jehobah.—K. Sha. 23:14.

16 Bai kamata mu riƙa tsabtace Majami’ar Mulki a lokacin da muka ga dama kawai ba. Ya kamata kowane rukunin dattawa su tsara yadda za a riƙa tsabtace ta kuma su tabbata cewa akwai isashen kayan aiki don tsabtace Majami’ar Mulki. Ya kamata a yi shara bayan kowane taro, amma akwai wasu abubuwa da ake tsabtacewa lokaci-lokaci. Saboda haka, ya kamata a bi tsari mai kyau don a riƙa yin waɗannan abubuwa. Ya kamata dukan ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya su ba da haɗin kai don tsabtace Majami’ar Mulki.

MU RIƘA KULA DA WURIN IBADARMU

17, 18. (a) Mene ne muka koya daga yadda mutanen Jehobah a dā suka kula da haikali? (b) Me ya sa ya wajaba mu kula da Majami’ar Mulki?

17 Bayin Jehobah suna yin iya ƙoƙarinsu don su riƙa yin gyare-gyare a Majami’ar Mulki. Alal misali, Sarki Jehoash na Yahuda ya ba da umurni cewa firistoci su yi amfani da gudummawa da aka ba da a gidan Jehobah don “a gyara duk inda ake bukatar gyara a haikalin.” (2 Sar. 12:4, 5, Littafi Mai Tsarki) Bayan shekaru 200, Sarki Josiah ya yi amfani da gudummawa da aka ba da don a yi gyare-gyare a haikali.—Karanta 2 Labarbaru 34:9-11.

18 An sami rahoto daga ofisoshin Shaidun Jehobah da ke wasu ƙasashe cewa mutane ba sa mai da hankali ga yin gyare-gyare ko kuma kula da gine-ginen Majami’ar Mulki. Wataƙila wasu a waɗannan ƙasashen ne suka san yadda ake yin aikin. Ko kuma ba su da isashen kuɗin yin gyare-gyare. Amma idan muka yi watsi da yin gyare-gyare a Majami’ar Mulki, ginin zai soma lalacewa kuma mutane ba za su ɗauki bautarmu da muhimmanci ba. Amma, idan ’yan’uwa suka yi iya ƙoƙarinsu don su kula da Majami’ar Mulki, hakan zai sa a yabi Jehobah. Ƙari ga haka, zai sa a riƙa amfani da gudummawar da ’yan’uwa suke bayarwa yadda ya dace.

Wajibi ne mu riƙa kula da tsabtace Majami’ar Mulki (Ka duba sakin layi na 16 da 18)

19. Mene ne ka ƙudura niyyar yi game da gine-ginen da muke amfani da su don bauta ta gaskiya?

19 Majami’ar Mulki gini ne da aka keɓe ga Jehobah. Saboda haka, ba mallakar wani mutum ko kuma wata ikilisiya ba. Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da wurin da muke bauta wa Jehobah. Dukan ’yan’uwa da ke cikin ikilisiya za su iya ba da haɗin kai don su daraja wuraren da muke bauta ta wajen ba da gudummawa don a ƙara gina wasu Majami’un Mulki, da kuma ba da lokacinsu da kuzarinsu don su kula da kuma tsabtace su. Idan muka saka hannu a yin waɗannan abubuwan, muna nuna himma a bautar Jehobah kamar yadda Yesu ya yi.—Yoh. 2:17.

^ sakin layi na 2 A wannan talifin, an mai da hankali ga Majami’un Mulki, amma ƙa’idodin da aka ambata a ciki sun shafi Majami’un Manyan Taro da kuma wasu wuraren da ake amfani da su don bauta ta gaskiya.