Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

JenkoAtaman/stock.adobe.com

KU ZAUNA A SHIRYE!

Dalilan Kasancewa da Bege a 2023—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Dalilan Kasancewa da Bege a 2023—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Yayin da muka shiga shekara ta 2023, muna yi wa kanmu da iyalanmu fatan alheri. Me ya sa za mu rika wannan fatan alheri?

Littafi Mai Tsarki yana sa mu kasance da bege

 A cikin Littafi Mai Tsarki akwai labari mai dadi cewa matsalolin da muke fuskantar yanzu na dan lokaci ne kuma ba da dadewa ba za a kawar da su. An rubuta Littafi Mai Tsarki “domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya ta wurin. . . karfafawa wadanda Rubutacciyar Maganar Allah sukan ba mu.”Romawa 15:4.

Kasancewa da begen da zai taimaka maka a yanzu

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bege “kamar anka take ga rai.” (Ibraniyawa 6:19, Littafi Mai Tsarki) Wannan begen yana iya sa mu jimre da matsalolin da muke fuskanta a yanzu, da kasancewa da raꞌayin da ya dace kuma mu yi abin da zai sa mu rika farin ciki. Alal misali:

Ka karfafa begenka

 Mutane da yawa suna sa rai cewa abubuwa za su gyaru a duniya, amma ba su da tabbaci ko hakan zai taba faruwa ba. Alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki za su cika. Me ya sa? Domin Jehobah Allah a da kansa wanda “ba ya ƙarya” ne ya yi wadannan alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. (Titus 1:2) Jehobah ne kadai yake da ikon cika dukan alkawuransa, zai iya yin duk abin da “ya ga dama.”—Zabura 135:5, 6.

 Muna gayyatarka ka zo ka amfana daga wannan begen da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Za ka iya karfafa begenka ta wajen ‘bincika’ Nassosi sosai. (Ayyukan Manzanni 17:11) Ka bincika da kanka ta wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da muke yi da mutane kyauta. Ka soma shekarar 2023 da sa rai cewa abubuwa za su gyaru a nan gaba!

a Jehobah ko Yahweh ne sunan Allah.—Zabura 83:18.