Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 121

Mu Rika Kame Kanmu

Mu Rika Kame Kanmu

(Romawa 7:​14-25)

  1. 1. Muna son Allah Jehobah sosai,

    Amma wajibi ne mu kame kanmu.

    Sha’awar jiki matsala ce

    Bin dokar Allah na ba da rai.

  2. 2. Shaiɗan na jarabtar mu koyaushe.

    Ajizanci na sa jimrewa wuya,

    Amma Allah na taimakon mu.

    Muna godiya ga Allahnmu.

  3. 3. Mutane za su ɗaukaka Allah

    Domin halayenmu da ayyukanmu.

    Sai mu ƙudura niyyar cewa

    Duk za mu riƙa kame kanmu.

(Ka kuma duba 1 Kor. 9:25; Gal. 5:23; 2 Bit. 1:6.)