Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotunan Biritaniya na 3 (Satumba 2016 Zuwa Fabrairu 2017)

Rumbun Hotunan Biritaniya na 3 (Satumba 2016 Zuwa Fabrairu 2017)

A wannan rumbun hotunan, za ka ga yadda aka gudanar da aiki a sabon ofishin Shaidun Jehobah a Britaniya a tsakanin Satumba 2016 zuwa Fabrairu 2017.

13 ga Satumba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

Motar tona rami na zuba kasa a cikin tifa. Don a soma shirin ginin, an tona kasa a filin kuma an kai shi wani gefe dabam.

15 ga Satumba, 2016​—Sashen gyare-gyare

Masu aiki a fannin lantarki sun samo wayoyin aiki. Za a yi amfani da wannan wurin don ofisoshi da kuma wurin cin abinci a lokacin da ake gina wannan sabon ofishin Shaidun Jehobah, kuma wurin ba shi da nisa.

19 ga Satumba, 2016​—Wajen da Ake Aiki

Yadda tsarin hanyoyi zuwa Wajen da Ake Aikinn yake ke nan idan a duba daga sama. A ta hagu kuma an fara shirin gina lambu da tafki, tare da wurin shakatawa domin mazaunan wurin da kuma baki.

3 ga Nuwamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

An farfashe kankare da aka tara a Wajen da Ake Aikin kuma an sake yin amfani da shi don gina hanyoyi a wurin

4 ga Nuwamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

A ta gaba kuma za a ga ma’aikata suna gina hanyoyi na dan lokaci da na dindindin. Sun yi amfani da farar kasa, domin tana sa hanyar ta yi karfi sosai. Ta hannun damar hoton kuma za a ga wata na’urar gyara hanya da ke matse kasa kafin a shimfida kwalta.

5 ga Nuwamba, 2016​—Bikin kaura zuwa sabuwar ofishin Shaidun Jehobah

Masu aikin sun sami labari daga daya cikin wuraren bukukuwa 18 wanda Construction Project Committee suka shirya a cikin Birtaniya da kuma Ireland. Shaidu fiye da 15,000 ne suka halarci bukukuwan, kuma yawancinsu sun ba da kansu domin aikin.

28 ga Nuwamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

Masu gyarar shimfidar wuri suna baza dusar katako kewaye da itacen willow da aka shuka. Wannan daya ne daga cikin itatuwa fiye da 700 da aka shuka a wurin. An yi wannan tafki domin ya rage karfin gudun ruwa idan an yi ambaliya, ya kuma tare ruwan sama sai kuma daidaita yadda ruwan zai gudu yadda ya kamata.

5 ga Disamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

An kara kuzari a aikin tonar kasa a daidai lokacin da an kusa kammala aikin don an yi hunturu a ranar. A duka duka dai, ’yan kwangila sun haka kuma diba kasa kusan mita 160,000​wanda zai cika tifofi fiye da10,000.

6 ga Disamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

Masu aikin gyarar shimfidar kasa suna shirya kasan domin yin shuki da zai zama mahani tsakanin lambun. An shuka irin itatuwa dabam-dabam 11 da kuma wasu irin shuke shuke 16 a ciki da kuma kewaye da shi, kuma daga yankin ne aka samo su duka.

19 ga Disamba, 2016​—Masauki

Ta hagu kuma, za a ga inji yana tona inda za a kafa tushen ginin. Da farko dai na’urar tana tona rami cikin kasan kadan kadan. Sai kuma, a zuba kankare cikin ramin yayinda ake zare na’urar. A karshe kuma, kamar yadda aka gani a tsakiyar hoton, ’yan kwangila suna saka karafuna cikin kankaren domin su kammala tushen ginin. An saka karafuna fiye da 360 cikin tushen ginin gidajen zaman.

29 ga Disamba, 2016​—Wajen da Ake Aikin

Cikin sanyin safiya, mai aikin famfo na hada hanyar ruwa da zai tallafa ruwa wa ofisoshin da aka gina na dan lokaci.

16 ga Janairu, 2017​—Wajen da Ake Aikin

Na’urar tona kasa ya tara kasa daga tafkin da aka haka a gefen filin. Yawancin tafkunan nan suna da matsaloli kuma suna bukatar a gyara su. Gyara mai kyau da aka yi wa tafkunan zai tsare su daga yashewa kuma ya rage kasada ta ambaliya. An kaura da kifaye fiye da 2,500 zuwa tafkunan da ke Wajen da Ake Aikin kafin a soma aikin gyarar.

17 ga Janairu, 2017​—Gidajen zama

Yadda Wajen da Ake Aikin yake kenan idan an kalle shi daga sama ta gabas. Daga gaba hoton ya nuna an soma tushen gina gidajen zama biyu. Ana iya ganin kasan da aka tara a hannun daman hoton ta kasa. Ta hagu kuma, an riga an zuba kankare. A tsakiyar hoton, na’urar tona kasa tana haka rami don saka karfen gini.

23 ga Janairu, 2017​—Sashen gyare-gyare

Daya daga cikin masu aiki yana hada kofa a Wurin Zaman Baki kafin a yi fenti. Baki za su iya su tsayawa daga nan kuma su ga dalla-dalla yadda aikin ke cin gaba.

14 ga Fabrairu, 2017​—Masauki

An sanya karfen da zai rike na’urar ɗaukan kaya. Wannan na’ura mai tsawon mita 40 zai iya daga kaya mai nauyin tan 18.

15 ga Fabrairu, 2017​—Masauki

An yanyanke karafunan da ke cikin kankaren daidai yadda ake bukatarsa. Yayin da ake zuba kankare zai rufe duk karfen da ke waje.

17 ga Fabrairu, 2017​—Wajen da Ake Aikin

Masu aikin lantarki sun sa alamun JW.ORG guda biyu a gefen bangon hanyar shigar ginin.

17 ga Fabrairu, 2017​—Wajen da Ake Aikin

An kammala hanyar shiga da fita da ake yawan amfani da ita. A sama ta hagu, an saka wasu sababbin alamun JW.ORG da ke sanar da ofishin Shaidun Jehobah. In an kammala shuke-shuken da ke lambun tare da tafkin za su sa hanyar shiga ta yi kyaun gani.

24 ga Fabrairu, 2017​—Gidajen zama

Tower crane yana kewaye filin da za a gina gidajen zama hudu cikin biyar da ake so a gina. A gaba, ’yan kwangila na zuba kankare a inda za a dinga ajiye motoci a karkashin wani gini. An saka karafuna, domin gina bangon.