Koma ka ga abin da ke ciki

Sakon da Ya Karfafa Mutane a Gasar Tour de France

Sakon da Ya Karfafa Mutane a Gasar Tour de France

An yi gasar tseren keke ta Tour de France na 103 a ranar 2 zuwa 24 ga Yuli, 2016. A shekara ta 2015, an kai hare-haren ta’addanci a kasar Faransa kuma an hallaka mutane fiye da 100. Sa’an nan a lokacin da ake bikin ranar hutun kasa a ranar 14 ga Yuli, 2016, wani dan ta’ada ya tuka mota kuma ya buga mutane da suka zo kallon wasan da ake yi da wuta a birnin Nice. Harin ya hallaka mutane 86 kuma wasu da dama sun ji ciwo.

Yayin da ake fama da bakin ciki da kuma zaman dardar a kasar, Shaidun Jehobah sun shirya yadda za su kawo sakon da zai karfafa mutanen kasar Faransa da suke cikin tsaka mai wuya. Sai suka tsaya da amalanken yin wa’azi a wuraren da ake yin gasar Tour de France. Shaidun Jehobah fiye da 1,400 ne suka ba da kansu don su taimaka a yin wannan aikin. Kuma sun rarraba littattafai fiye da 2,000 wa mutanen da suke neman amsoshin tambayoyi da suka fi muhimmanci.

‘A Kowane Wuri Ne Kuke?’

Wadanda suke bin ‘yan gasar zuwa garurruka sun yi mamakin ganin Shaidun Jehobah a wurare da yawa. Sau da yawa wani memban masu kula da Tour de France ya yaba wa Shaidun Jehobah don yadda suke yin aikinsu da tsari, kuma ya ce: “Kowane wuri ne kuke? Don ina ganinku a duk inda ake gasar!” Ga abin da wasu ‘yan kallo suka ce: “Shaidun Jehobah suna nan ma!” bayan an soma gasar da ‘yan kwanaki, wani direban bas ya ki ya karba warka don a cewarsa ya riga ya karbi guda hudu!

Ganin Shaidun Jehobah a ko’ina a wuraren gasar ya burge wasu mutane har sun karbi littattafanmu. Wani ma’aikacin gidan talabijin da ke yada labaran wasanni ya ce ya ga Shaidun Jehobah shekara da ta wuce a wurin gasar Tour de France. Amma wannan shekarar, sai ya je ya dauka littafin nan Asirin Farinciki na Iyali don littafin na dauke da bayanai masu muhimmanci da yake so. Bayan ya dan karanta littafin a motarsa, sai ya gaya wa abokan aikinsa inda ya samo littafin, sai su ma suka je suka karbi nasu littattafan.

Sakon Mai Ban Karfafa

Wasu mutane da suka zo wurin gasar sun gaya ma Shaidun Jehobah irin matsalolin da suke fama da su. Wata matashiya ta ce ta rasa abin da za ta yi har ta soma tunanin zuwa hanyar jirgin kasa don ta kashe kanta. Bayan da aka yi mata wa’azin da ya karfafa ta sai ta daina tunanin kashe kanta. Wata mata ta gaya ma wasu Shaidun Jehobah cewa, “Ku ci gaba da aikin nan don yana da amfani!”

Wani mutum da yake tafiya da sanda, ya ce yana tsoron baki sosai, amma ya yarda wata ‘yar’uwa ta taimaka masa don irin tufafin da ta saka ya dace. Ga abin da ya ce: “Na so irin tufafin da kika saka kuma kina da fara’a, hakan ya karfafa ni sosai.”