Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Sasanta da Mahaifina

Na Sasanta da Mahaifina
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1954

  • KASAR HAIHUWA: Filifin

  • TARIHI: Na daina cudanya da mahaifina azzalumi

RAYUWATA A DĀ

 Mutane da yawa suna zuwa yawon bude ido a wani sanannen wuri da ruwa ke gangarowa kusa da garin Pagsanjan a kasar Filifin. A wurin ne mahaifina mai suna Nardo Leron ya yi girma, kuma su talakawa ne sosai. Ganin yadda gwamnati da ’yan sanda suke cin hanci da rashawa da kuma yadda ake yin hakan a wurin aikinsa ya sa shi bakin ciki da fushi.

 Iyayena sun yi aiki sosai don su biya bukatun yaransu guda takwas. Sukan dade ba su dawo gida ba domin suna kula da gonaki a tuddai. A yawancin lokaci ni da yayana mai suna Rodelio ne muke kula da kanmu, kuma sau da yawa ba mu da abincin da za mu ci. Ba ma yawan samun zarafin yin wasa a lokacin da muke yara. Kowannen mu yana soma aiki sosai a gona sa’ad da ya kai shekara bakwai, mukan ɗauki buhun kwakwa mai nauyi muna hawan kan tuddai. Idan ba mu iya daga kayan ba saboda da nauyi, ana tilasta mana mu rika jan kayan.

 Mahaifinmu yakan yi mana dūka sosai, amma mun fi bakin ciki idan muka ga yadda yake dūkan mahaifiyarmu. Mun yi kokari mu sa shi ya daina hakan, amma ya ki dainawa. Ni da yayana Rodelio mun kulla cewa za mu kashe mahaifinmu sa’ad da muka yi girma. Na yi fatan samun mahaifi da zai rika kaunar mu!

 Na bar gida sa’ad da nake dan shekara 14, domin ina bakin ciki da kuma fushi don yadda mahaifina yake zaluntar mu. Ina kwana a kan titi kuma na soma shan wi-wi. Daga baya, na soma tuka kwalekwale, ina kai masu yawon bude ido zuwa wurin da ruwa ke gangarowa da na ambata dazu.

 Na shiga makarantar jami’a da ke Manila bayan wasu shekaru. Amma ba ni da lokacin yin nazari sosai domin nakan koma garin Pagsanjan a karshen mako don aiki. Kamar dai rayuwata ba ta da ma’ana, kuma tabar wi-wi ba ta hana ni yin alhini kamar dā. Sai na soma shan kwayoyi masu karfi sosai, kamar hodar iblis da kuma tabar heroin. A yawacin lokaci, shan kwayoyi yakan sa mutum ya soma yin lalata. Kari ga haka, ina ganin talauci da rashin adalci da wahala a ko’ina. Na tsani gwamnati don ina ganin su ne suke jawo wadannan matsalolin. Na tambayi Allah, “Me ya sa abubuwan nan suke faruwa a rayuwa?” Amma addinai dabam-dabam da na je ba su iya ba ni amsoshin ba. Sai na kara shan kwayoyi don in boye bakin cikin da nake yi.

 A shekara ta 1972, dalibai a kasar Filifin sun soma yin zanga-zanga. Na bi su yin wani zanga-zanga, kuma an yi kashe-kashe sosai. An kama mutane da yawa kuma bayan watanni, sai gwamnati ta kafa doka cewa sojoji ne za su rika kula da harkokin jama’a a kasar.

 Na soma kwana a kan titi kuma domin ina jin tsoron hukumomi, da yake ina cikin wadanda suka yi zanga-zangar. Don in sami kudin sayan kwayoyi, sai na soma sata da yin lalata da mutane masu kudi da kuma baki. Ban damu ba ko zan mutu ko kuma zan rayu.

 A wadannan lokutan ne mahaifiyata da kanena suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Mahaifina ya yi fushi sosai kuma ya kona littattafansu. Amma sun nace kuma suka yi baftisma.

 Wata rana, wani Mashaidi ya nuna wa mahaifina alkawarin da Allah ya yi a cikin Littafi Mai Tsarki cewa a nan gaba za a yi adalci a dukan duniya. (Zabura 72:​12-​14) Hakan ya ratsa zuciyar mahaifina kuma ya tsai da shawara zai kara yin bincike da kansa. A cikin Littafi Mai Tsarki, ya koya cewa Allah ya yi alkawarin kafa gwamnatin da za ta biya bukatunmu. Ban da haka, ya koyi abin da Allah yake so magidanta da ubanni su rika yi. (Afisawa 5:28; 6:⁠4) Bayan dan lokaci, sai shi da dukan ’yan’uwana suka zama Shaidu. Ni ban san abin da yake faruwa ba da yake ina nesa da gida.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Na kaura zuwa kasar Ostareliya a shekara ta 1978. Amma ba ni da kwanciyar rai har a wannan kasar da mutane suke da arziki kuma suna zaman lafiya. Na ci gaba da shan giya sosai da kuma shan kwayoyi. A wannan shekarar, sai Shaidun Jehobah suka zo gidana. Na yi farin ciki don sun nuna mini a cikin Littafi Mai Tsarki cewa za a yi zaman lafiya a duniya, amma ban saki jiki da su ba don ban san su sosai ba.

 Bayan haka, na koma kasar Filifin kuma na yi ’yan makonni. ’Yan’uwana sun gaya mini cewa mahaifina ya canja halinsa, amma har ila ina fushi da shi kuma na yi kokarin guje wa duk wani abin da zai hada ni da shi.

 Kanwata ta nuna mini a cikin Littafi Mai Tsarki dalilin da ya sa ake shan wahala da kuma rashin adalci a duniya. Na yi mamaki cewa kanwata da ba ta san yadda rayuwar duniya take ba ta san amsa tambayoyina. Kafin in tafi, mahaifina ya ba ni littafin nan Kana Iya Rayuwa Har Abada a Duniya. * Sai ya ce: “Ka daina neman amsoshi da kuma kwanciyar rai ta hanyoyin da ba su dace ba. Wannan littafin zai taimaka maka ka sami amsoshin da kake nema.” Sai ya karfafa ni in nemi Shaidun Jehobah a Ostareliya.

 Na bi shawarar mahaifina kuma na je wata Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah da ke kusa da gidana a birnin Brisbane. Na amince a rika nazarin Littafi Mai Tsarki da ni a kai a kai. Annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki kamar wadanda suke cikin Daniyel sura 7 da Ishaya sura 9 sun nuna mini cewa Mulkin Allah da ba a cin hanci ne zai soma sarauta a duniya a nan gaba. Na koyi cewa za mu more Aljanna a duniya. Ina so Allah ya amince da ni, amma na fahimci cewa ina bukatar in rika kame kaina idan na yi fushi da kuma daina shan kwayoyi da yin maye. Kari ga haka, ya kamata in daina yin lalata. Sai na rabu da budurwata da muke zaman dadiro kuma na daina shan kwayoyi. Yayin da nake kara dogara ga Jehobah, sai na yi addu’a ya taimaka mini in yi canje-canjen da suka dace.

 A hankali, na fahimci cewa abin da nake koya zai iya canja rayuwar mutum. Littafi Mai Tsarki ya ce idan muka kokarta, za mu dauki ‘sabon hali.’ (Kolosiyawa 3:​9, 10) Yayin da nake kokari in yi hakan, sai na fahimci cewa watakila da gaske ne cewa mahaifina ya canja halinsa. Maimakon in tsane shi, sai na so in sasanta da shi. Daga baya, na gafarta wa mahaifina kuma na daina rike shi a zuciya, don ina hakan tun ina yaro.

YADDA NA AMFANA

 Sa’ad da nake matashi, nakan yi cudanya da abokan banza. Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce gaskiya ne, abokan banza sun rude ni. (1 Korintiyawa 15:33) Amma na sami abokan kirki tsakanin Shaidun Jehobah, kuma sun taimaka mini in zama mutumin kirki. Kari ga haka, na sami matar kirki mai suna Loretta. A yanzu, muna koya wa mutane yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka musu.

Ina cin abinci tare da matata da abokanmu

 Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mahaifina ya zama irin mutumin da nake ganin ba zai taba zama ba, ya zama miji mai kauna da kuma mai saukin kai. Kuma ya zama Kirista mai son zaman lafiya da mutane. Sa’ad da na hadu da mahaifina bayan na yi baftisma a shekara ta 1987, sai ya rungume ni a lokaci na farko a rayuwata!

 Fiye da shekara 35, mahaifiyata da mahaifina sun ci gaba da koya wa mutane sakon da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Mahaifina ya zama mutum mai kwazo da ke taimaka wa mutane. A wannan lokacin, na mutunta shi sosai kuma na kaunace shi. Ban da haka, na yi alfaharin cewa ni dansa ne! Ya mutu a shekara ta 2016, nakan tuna da shi da farin ciki, na san cewa mun yi canje-canje sosai a rayuwarmu yayin da muka soma bin umurnin Littafi Mai Tsarki. Ban tsane shi kuma ba ko kadan. Kuma ina farin ciki cewa na sami Uba, wato Jehobah wanda ya yi alkawari cewa zai kawar da dukan abubuwan da ke jawo matsaloli a iyalai a ko’ina.

^ sakin layi na 12 Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi, amma an daina buga shi.