Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shin Za Mu Iya Sanin Abin da Zai Faru A Gaba Ta Wurin Ilimin Taurari da Dūba?

Shin Za Mu Iya Sanin Abin da Zai Faru A Gaba Ta Wurin Ilimin Taurari da Dūba?

ILIMIN TAURARI

Ilimin taurari wani irin bincike ne ko dūba da masanan taurari suke yi ta yin amfani da taurari da wata da kuma duniyoyi kuma su yi da’awa cewa hakan na shafan yadda mutane suke rayuwa a duniya. Waɗannan masanan suna cewa tsayuwar abubuwan nan a lokacin da aka haifi mutum ne suke nuna halin mutumin da kuma abin da zai faru da shi a nan gaba.

Ko da yake ilimin taurari ya samo asali ne daga Babila ta dā, har wa yau mutane suna yin sa. Akwai mutane da yawa da suka gaskata cewa za su iya sanin abin da zai faru a nan gaba daga wurin masu ilimin taurari. Amma za mu iya gaskata da abin da masu ilimin taurari suke faɗa kuwa? A’a. Bari mu ga dalilin da ya sa muka ce hakan.

  • Duniyoyi da kuma taurari ba su da wani iko da yake shafan mutane kamar yadda masanan taurari suke faɗa.

  • Sau da yawa, abubuwan da suke faɗa cewa za su faru za su iya shafan kowa.

  • Hasashen da masanan taurari suke yi a yau bisa abubuwan da mutane suka gaskata da su a dā ne cewa duniyoyi suna kewaye doron ƙasa. Amma a gaskiya, duniyoyi suna kewaye rana ce ba doron ƙasa ba.

  • Abubuwan da masanan taurari dabam-dabam suke faɗa game da mutum ɗaya ba sa jituwa da juna.

  • Masanan taurari sun ce waɗannan alamun ne suke nuna yadda halin mutum zai zama. Amma gaskiyar ita ce, halin mutanen da aka haife su a rana ɗaya yakan bambanta. Ranar da aka haifi mutum ba ta da wani alaƙa da halinsa. Maimakon su ɗauki mutum yadda yake, masanan taurari sukan yi hasashe ko kuma su ƙaga wasu abubuwa game da halinsa. Hakan ɓata suna ne, ko ba haka ba?

MASU DŪBA

Tun dā can mutane suna zuwa wurin masu dūba don su faɗa musu abin da zai faru a nan gaba. Wasu masu dūba suna neman ma’anar abubuwa ta yin amfani da kayan cikin dabbobi da na mutane har da yadda zakara yake cin abinci. Wasu kuma sukan yi hasashe bisa ganyen shayi da kofi. A yau suna amfani da katin tarot da zuba wuri da kuma wasu abubuwa don su faɗi ko “san” abin da zai faru da mutum a nan gaba. Shin da gaske ne cewa masu dūba suna faɗan ainihin abin da zai faru a nan gaba? A’a. Bari mu bincika wannan batun.

Rashin jituwa da juna. Hasashen da mutane suke yi game da nan gaba da kuma hanyoyin da suke amfani da su ba sa jituwa da juna sam. Ko da sun yi amfani da hanya ɗaya wajen yin hakan, abin da suke faɗa cewa zai faru ba iri ɗaya ba ne. Alal misali, idan mutum ya ce wa masu dūba biyu su “karanta” katin tarot iri ɗaya don su gaya masa abin da zai faru da shi, ai ya kamata su faɗi abu ɗaya, ko ba haka ba? Amma a yawancin lokaci, abin da suke faɗa dabam-dabam ne.

Mutane suna shakkar hanyoyin da masu dūba suke amfani da su. Wasu masu kushe su sun ce kati ko zuba wuri da suke yi ba su da ikon yin wani abu. Alal misali, mai dūba da ya ƙware yakan yi wa mutumin da ya zo wurinsa tambayoyi da yawa kuma ya lura da bakin mutumin da yadda yake magana don ya gano wasu abubuwa game da mutumin. Bayan haka, mutumin zai ɗauka cewa bokan ya san abin da yake damunsa. Amma a kashin gaskiya, mutumin ne ya sa bokan ya san abubuwan nan ba tare da saninsa ba. Kuma idan masu dūba suka yi wannan dabarar, mutanen da suka zo wurinsu sukan ba su kuɗi mai yawa sosai.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA GAYA MANA

Neman sanin abin da zai faru a nan gaba da kuma hasashe yana ƙarfafa koyarwar ƙaryan nan cewa an riga an ƙaddara abin da zai faru da mu. Amma hakan gaskiya ne? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa muna da ’yancin zaɓan abin da za mu yi imani a kai da kuma abin da muke so mu yi a rayuwa kuma hakan ne yake shafan rayuwarmu a nan gaba.​—Yoshuwa 24:15.

Bayin Allah suna da dalilai masu kyau na ƙin dūba don sun san cewa Jehobah ya tsani kowane irin sihiri. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba za a sami waninku da zai . . . zama mai duba, ko mai maita, ko mai dabo, ko mai sihiri, ko boka, ko mai sha’ani da ruhohi, ko mai haɗa kai da ruhohin matattu ba. Gama duk wanda ya aikata waɗannan abubuwa ya zama abin ƙyama ne ga Yahweh.” a​—Maimaitawar Shari’a 18:​10-12.

a Sunan “Mafi Ɗaukaka a dukan duniya” shi ne Yahweh ko Jehobah.​—Zabura 83:18.