Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Masu Saukin Kai Za Su Gāji Kasar”

“Masu Saukin Kai Za Su Gāji Kasar”

Yawancinmu mun ga yadda ake nuna wa mutane rashin adalci da kuma yadda ake cin zalin mutane masu adalci. Shin akwai lokacin da za a daina rashin adalci da mugunta kuwa a duniya?

Littafin Zabura 37 ya ba da amsar kuma ya ba mu shawara mai kyau game da hakan. Ka yi la’akari da abin da ya faɗa a tambayoyi na gaba.

  • Yaya za mu yi sha’ani da waɗanda suke wulaƙanta mu?​—Aya ta 1 da 2.

  • Me za a yi wa mugayen mutane?​—Aya ta 10.

  • Wace albarka za a yi wa mutane masu adalci?​—Aya ta 11 da 29.

  • Me ya kamata mu yi yanzu?​—Aya ta 34.

Kalaman littafin Zabura 37 sun nuna dalla-dalla begen waɗanda suka ‘yi sauraro ga Ubangiji, suka kiyaye tafarkinsa.’ Shaidun Jehobah za su ji daɗin taimaka maka ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ka san yadda za ka tsai da shawarar da za ta sa kai da danginka ku sami albarka a nan gaba.