Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki

Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki

(Zabura 16:11)

Ka Saukar:

  1. 1. Allah ne ya yi taurari

    Da ke haskawa

    Ya yi dare da rana don

    Yana kaunar mu

    Shi ya halicci duniya,

    Kuma duk abin da ya yi

    Sun sa shi murna.

    (AMSHI)

    Muna farin ciki sosai,

    Domin ka yi alkawari,

    Za ka kawo aljanna.

    Amma abu mafi girma

    Shi ne kaunarka gare mu.

    Kai kadai ke sa mu yi

    Farin ciki kullum.

  2. 2. Jehobah halittunka na

    Da ban sha’awa​—

    Muna gani, muna taba

    Da kuma jin su.

    Kana biyan bukatunmu

    Ka ba mu begen rayuwa

    Cikin aljanna.

    (AMSHI)

    Muna farin ciki sosai,

    Domin ka yi alkawari,

    Za ka kawo aljanna.

    Amma abu mafi girma

    Shi ne kaunarka gare mu.

    Kai kadai ke sa mu yi

    Farin ciki kullum.

  3. 3. Fansar Yesu Kristi

    Na sa mu farin ciki.

    Hadayarsa ta ceto mu

    Shi ya sa muke yin murna.

    (AMSHI)

    Muna farin ciki sosai,

    Domin ka yi alkawari,

    Za ka kawo aljanna.

    Amma abu mafi girma

    Shi ne kaunarka gare mu.

    Kai kadai ke sa mu yi

    Farin ciki kullum.

    (AMSHI)

    Muna farin ciki sosai,

    Domin ka yi alkawari,

    Za ka kawo aljanna.

    Amma abu mafi girma

    Shi ne kaunarka gare mu.

    Kai kadai ke sa mu yi

    Farin ciki kullum.

    Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki.

(Ka kuma duba Zab. 37:4; 1 Kor. 15:28.)