Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Muna da Hadin Kai

Muna da Hadin Kai

Ka Saukar:

  1. 1. Mun ga gari ya yi duhu.

    Mun taba shaida hakan.

    An soma tsananta mana

    Ba bakon abu ba ne.

    Za mu yi karfin zuciya,

    Babu gudu, ba tsoro.

    Mun san Allahnmu, Jehobah,

    Za ya kāre dukanmu.

    (AMSHI)

    Mu kamar tsintsiya muke,

    Mai madauri daya tak.

    Ba za mu ja da baya ba,

    Don Jehobah yana nan,

    Don Jehobah yana nan.

  2. 2. Mun yi imani da Allah,

    Don shi Madaukaki ne.

    Jehobah yana da iko

    Kuma shi mai kauna ne.

    Zai tuna da mutanensa,

    Zai taimake su sosai.

    Zai kunyantar da makiya,

    Domin mu bayinsa ne!

    (AMSHI)

    Mu kamar tsintsiya muke,

    Mai madauri daya tak.

    Ba za mu ja da baya ba,

    Don Jehobah yana nan.

  3. 3.

    Mun yi tsayin dāka,

    Ba ma tsoron makiya.

    Mun riga mun ba da kanmu

    Ga Jehobah Allahnmu.

    (AMSHI)

    Mu kamar tsintsiya muke,

    Mai madauri daya tak.

    Ba za mu ja da baya ba,

    Don Jehobah yana nan,

    Don Jehobah yana nan.